2023: Zan Bayyana Aniyata Ta Takarar Shugaban Ƙasa A Lokacin Da Ya Dace— Kwankwaso

325

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai bayyana aniyarsa ta yin takarar Shugaban Ƙasa a lokacin da ya dace a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP.

Kwankwaso ya ce a halin yanzu abin da ya sa a gaba shi ne ya taimaka wajen ƙarfafa PDP ta hanyar Ɗarikar Kwankwasiyya ta fannin ilimantarwa, samar da ayyukan yi daga nan zuwa 2023 da ma gaba.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja lokacin da wasu ƙungiyoyi suka kai masa ziyara don nuna goyon bayansu gare shi da kuma Ɗariƙar Kwankwasiyya.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su girmama muradun sauran masu sha’awar yin takarar Shugaban Ƙasa a PDP.

Kwankwaso ya yi takarar Shugaban Najeriya a 2019, sai dai ya sha kaye a hannun tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a yayin zaɓen fidda gwani.

Kwankwaso ya siffanta Atiku, tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da sauransu a matsayin ‘yan uwa kuma abokan ci gaba a wajen ‘yanto Najeriya da kuma ɗora ta a turbar ci gaba.

“Ina shawartar dukkan magoya bayana a PDP da kuma Ɗariƙar Kwankwasiyya da sauran abokan arziƙi kada su zagi ko ci mutuncin wani mai son yin takara ko jagoran jam’iyya a madadina”, yana mai ƙarawa da cewa jam’iyyar ita ce sama da kowa.

“Bai kamata mu yi wasu abubuwa da za su zubar da kimar wani jagora ba, ko kuma abubuwan da za su haifar da rashin haɗin kai a muƙaman jam’iyyar. Duk wanda ya yi haka to ba wakilta ta yake yi ba”, in ji Kwankwaso.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan