Yadda aka fara yiwa gwamnonin Najeriya allurar riga-kafin cutar Korona

100

A cigaba da allurar riga-kafin cutar Korona a yau Laraba gwamnonin jihohin Jigawa da Kaduna da kuma Neja ne aka yi musu allurar riga-kafin.


Tun da farko gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya wallafa hotunan yadda jami’an kiwon lafiya na jihar ta Neja su ka yi masa allurar riga-kafin shi da mataimakinsa.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello lokacin da ake masa allurar riga-kafin Korona

Haka kuma gwamna Nasiru El-Rufai an yi masa allurar riga-kafin tare da mataimakiyar sa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe.

Gwamna Basiru El-Rufai a lokacin da ake masa allurar riga-kafin Korona

Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa bayan da aka yi masa allurar riga-kafin ya samu kimanin mintuna ashirin yana zaune domin ya tabbatarwa da al’ummar jihar Kaduna cewa allurar riga-kafin ba ta da wata illa ga lafiyar bil’adama.

Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a lokacin da ake mata allurar riga-kafin Korona


Shi ma gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa an yi masa allurar riga-kafin cutar ta Korona da shi da mataimakinsa a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Dutse.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a lokacin da ya ke karɓar allurar riga-kafin Korona


Allurar rigakafi kusan miliyan huɗu Najeriya ta karɓa daga wani ɓangare na rigakafi miliyan 16 da shirin COVAX ya tsara ba kasar nan.


Shirin dai na Covax ya shafi tabbatar da kowacce ƙasa a duniya ta samu na ta kason na rigakafin korona.


Haka kuma gwamnatin tarayya ta ce ta tsara yi wa akalla kashi 70 na ƴan Najeriya da suka cancanci a yi musu riga-kafin wato wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa sama a cikin shekaru biyu.


A bana Najeriya na fatan yi wa kashi 40 na ƴan kasarta rigakafin da kuma kashi 30 a 2022.

Najeriya ta kasance kasa ta uku a yankin Afrika Ta Yamma da suka ci moriya tallafin alluran riga-kafin karkashin shirin COVAX, baya ga Ghana da Cote D’Ivoire.

Wanne Mataki Za A Ɗauka Akan Wanda Bai Yadda An Yi Masa Riga-kafin Ba?

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona a Najeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya ƙasashen waje.

Mustapha wanda kuma shi ne sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan an yi wa Buhari da Osinbajo allurar rigakafin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan