Ban gudu daga Najeriya ba – Salihu Tanko Yakasai

19

Tsohon mataimaki na musamman kan kafafen yaɗa labarai ga gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya ƙaryata jita -jitar da ake yaɗawa akan cewa ya tsallaka ƙasashen Ƙetare kuma ba zai dawo ba har sai wa’adin mulkin shugaba Muhammad Buhari ya cika.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne a shafin sa na facebook, a yau Alhamis, a matsayin martani ga masu cewa ya bar Najeriya.

Na rubuta cewa zan yi tafiya bayan na isa inda zani yanzu, na kunna waya na ga ko ina a harabar shafukan sadarwa na zamani (social media) har da manyan jaridun kasar nan ya cika da labarin cewa wai na gudu daga kasar, wannan ba gaskiya bane kuma babu ma a inda maganar nan ta samu tushe. Hutu na je kuma zan dawo gida In Sha Allah, dan bana jin da wanda ya kai ni san zama a Kano, Abuja ma na kasa komawa da zama bare na bar kasar gaba daya”

Ya ƙara da cewa “Wannan ta sa dole manyan mu a ɓangaren aikin jarida da malamai na koyar da aikin jarida su yi nazari akan labarai irin wannan marasa tushe”


Na farko dai a dinga bincike kafin ayi labari irin wannan mara hujja, da sun tambayi ƴan uwana ko aminai na, da za su san hutu na tafi, ko kuma su yi hakuri idan na isa su tambaye ni na fada musu da kai na, kuma duk wanda ya sanni dama ya san ina da sha’awar zagaya duniya. Kawo yanzu na je ƙasashe 46, kuma buri na ne na je kusan duk manyan ƙasashen duniya, amma yawon buɗe ido ba komawa can da zama ba”

“Dan haka na ke kira da a kalli aikin nan kafin ya lalace gaba daya, a dinga tsawatar wa da duk wani dan jarida da yayi labari irin haka ba da hujja mai kwari ba, domin yana zubarwa da gidajen jaridun kima, sannan kuma yana kawo shakku akan wasu labari da zasu buga a gaba”

A jiya ne dai labarin barin Salihun Najeriya ya cika shafukan intanet, wanda har wasu na kallon hakan a matsayin tsananin adawa ga mulkin shugaba Buhari.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Oktobar shekarar bara ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da Salihu Tanko Yakasai kan wata suka da ya yi a shafin Twitter ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan