Kanu Nwanko ya ziyarci gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

181

Tsohon dan wasan Najeriya, kuma tsohon kyaftin ɗin kungiyar ƙwallon kafa ta Super Eagles, Nwankwo Kanu, ya ziyarci gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Nwankwo Kanu wanda ɗaya ne daga cikin fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka, ya baiwa Gwamna Yahaya Bello kyautar ƙwallon ƙafa da riga da kuma littafin tarihin rayuwarsa.

Ana kallon wannan ziyara ta Kanu na da nasaba da siyasa, la’akari da yadda ake ganin gwamna Yahaya Bello na da sha’awar yin takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan