Ganduje Na Yi Min Barazana Da Rayuwata— ‘Yar Gwagwarmaya

21

Ganduje Na Yi Min Barazana Da Rayuwata— ‘Yar Gwagwarmaya
Wata ‘yar gwagwarmaya kuma lauya, Sa’ida Sa’ad Bugaje ta ce Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da jami’an ‘yan sanda na Shiyya ta Ɗaya ta jihar Kano suna yi mata barazana da rayuwarta.

A wani saƙon ceton rai da ta tura wa jaridar Intanet, Solacebase, ranar Juma’a, ta ce ita da iyalanta suna ci gaba da rayuwa cikin tsananin tsoro tun 16 ga Satumba, 2020.

Jaridar Solacebase ta gano cewa Gwamna Ganduje yana yi wa ‘yar gwagwarmayar barazana sakamakon wani bidiyo da ta fitar kwanan nan inda ta zargi Gwamnan da yin ɗungushen wasu kuɗaɗen tallafin COVID-19.

Sanarwar da ‘yar gwagwarmayar ta fitar ta ce ranar 16 ga Satumba, jami’an ‘yan sanda daga Shiyya ta Ɗaya a jihar Kano sun je gidanta a Kaduna da nufin kama ta.

“Amma ba a ƙyale jami’an ‘yan sandan sun shiga harabar gidan ba saboda kana ganin su ka san suna zargi. Ba sa sanye da kaki, kuma suna ɗauke da bindigogi”, in ki Bugaje.

“Lokacin da muka bincike su dalilin kama ni, sai suka ce: “Idan kika je ofishin Shiyya na ‘Yan Sanda a Kano za a sanar da ke”. To saboda halin rashin tsaro da ake ciki da kuma garkuwa da mutane, sai na ƙi bin su saboda ba su ma da shaidar kame”.

“Sakamakon haka, lokacin da suka dawo ranar 18 ga Satumba, an faɗa min cewa sun shiga harabar gidan da ƙarfi saboda ba nan nan, suna nuna wata takardar umarnin kame mai ɗauke da kwanan 17 ga Satumba, wadda ta yi kama da ihu bayan hari”, ta ƙara haka.

Bugaje ta ce daga bayan nan an sanar da ita cewa saboda wancan bidiyo ne da ta yi a kan Gwamna Ganduje ne shi yasa ‘yan sanda suke yi mata barazana.

“Na yi mamaki saboda a ra’ayina, idan Ganduje yana da wani abu a game da bidiyon, zai iya tafiya kotu ni kuma zan shirya don kare kaina, ya ƙi yin haka sai cin mutunci da tsoratar da ni da iyalina a ko’ina da ‘yan sanda.

“Na samo umarnin kotu da ya hana ‘yan sanda da Ganduje su ci min zarafi da kuma tsoratar da ni da iyalina, amma ƙememe sun ƙi bin wannan umarni”, in ji ta.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Wai kowa yatashi gwagwar mayar sa a yadda suke cewa batsayawa ko ina sai akan gwamnan Kano sbd kun rainashi kuma kusan ba wata jiha da ake irn wannan idan ba kano ba Idan har kun isa kuje kuyi gwagwarayar akan wadana suke da hannu a ta’addancin da ake a Kasa mana kokuma kuyi gwagwar mayar kwato mana yancin mu na cimana mutuncin da akeyi a yankin KUDU mana. Amma kun tsaya sbd tsabar kiyayya da siyasa akan gwamnan Kano sbd ba jam’iyyar ku yakeba

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan