Gwamna Bala Muhammad ya ziyarci attajiri Aminu Alhassan Dantata

45

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abfulkadir Muhammad ya ziyarci fitaccen attajirin nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Ƴan siyasa da masu neman mulki musamman ƴan arewacin Najeriya na kaiwa Aminu Alhassan Dantata ziyarar ban girma tare da neman tubarraki.

Idan za a iya tunawa dai ko a makon jiya sai da tsohon mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya akan harkokin majalisa, Honarabul Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya kaiwa attajirin ziyara, inda attajirin ya ɗauki nauyin karatun ƴaƴan talakawa guda 100 a sabuwar jami’ar Al- Istiqama da ke garin Sumaila a jihar Kano.

Turawa Abokai

1 Sako

Leave a Reply to Muhammad Saidu lokuja Sake amsa

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan