Mungano Wanda Suka Damfari Hukumar JAMB Miliyan 10 – Farfesa Ishaq Olayede

110

‘Yan damfara sun yi kutse a shafin hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB, tare da kwashe kuɗaɗe kimanin miliyan 10 a cewar shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Olayede.

Olayede ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Laraba, 14 ga Afrilu 2021 inda ya ce ‘yan damfarar sun shiga shafukan ma’aikatan wucin gadi na hukumar inda suka sace Naira Miliyan 10 na alawus ɗinsu.

Ya ce hukumar ta bankaɗo asirin ‘yan damfarar ne bayan da aka gudanar da bincike wanda ya kai ga kama wani mai suna Sahabi Zubairu dake garin Tukum na jihar Taraba da kuma wasu da dama.

Oloyede ya yin da yake bayani ya bayyana cewa haƙiƙa gwamnati na buƙatar wannan kuɗi da ake bawa ma’aikatan wucin gadi, inda ya ce lamarin ne ya haifar da ƙalubalen da tsaikon da hukumar ke fuskanta.

Shugaban hukumar ta JAMB, ya kuma ƙara da cewa tuni an biya ma’aikatan wucin gadin, ya kuma tabbatar da cewa za’a kwato kuɗin da aka sace nan ba da jimawa ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan