Adabi: Na yi nadamar rera waƙar Abubakar Ladan – Aminu Alan Waƙa

206

Fitaccen mawaƙin nan Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waƙa, ya bayyana cewa ya yi nadamar rera fitacciyar waƙar nan ta marigayi Abubakar Ladan Zariya, inda ya rera ta a salo na zamani tare da kayan kiɗa na zamani da nufin zamanantar da waƙar.

Alan Waƙa ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar Blueprint akan dalilan da ya kai shi ga rera wakar a wani salon daban.

Tun da farko an yiwa Alan Waƙa tambayar cewa duk da wahalar da ka sha a wajen rerewa daga bayaninka na baya kamar ba ka ci moriyar waƙar ba? Sai Alan ya bayar da amsa haka kamar haka

To, ai daga cikin abubuwan da na yi a waƙa, ba don girmama shi malamin da ya saka ni na yi waƙar ba, to irin yadda iyalan Abubakar Ladan suka ɗauke ni da irin yadda suke kallo na a kan waƙar cewar na shiga cikin gadonsu, to da zan iya cewa shi ne, na yi da-na-sanin ban yi ba, domin a waƙa ba na shiga hurumin mutane, kuma duk abin da na yi zan yi ƙoƙarin na yi abin da ya dace da ni, amma wannan waƙar ba martabata ta ɗaga ba, martabar mahaifinsu ta ɗaga, saboda duk inda ya faɗi abu haka na ke faɗarsa kuma Ina gabatar da sunan sa cewar shi ne mai waƙar, shi ya rubuta ta”


Haka kuma Aminu Alan Waƙa ya ce duk da irin kashe kuɗin da ya yi masu yawan gaske amma sai gashi waɗanda ya kamata a ce sun yaba masa da wannan ƙoƙari sai ga shi su ne ke son ganin an saka shi a gidan yari.

Don haka idan akwai wani abu da na yi a ɓangaren fasaha kuma na yi da-na-saninsa, to wannan waƙar ce. Don na kashe kuɗina masu yawa, amma waɗanda ya kamata su ga na yi musu abin alfahari sune suke ƙoƙarin su ga sun tura ni a gidan yari; wai don suna tunanin na yi amfani da fasahar babansu. Don haka na yi da-na-sani da Allah wadai da aikin wannan waƙar da na yi”


Mawaƙi Aminu Alan Waƙa ya ce tun farko shugaban Majalisar Malamai ta jihar Kano ne ya buƙaci da zamanatar da waƙar la’akari da irin alfanunta ga tarihin nahiyar Afirka.


Abin ya samo asali shi ne, Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ne ya same ni a ofishina ya ce, buƙatarsa ce ta kawo shi, ya ba ni CD na waƙar Abubakar Ladan ya ce, “Ni masoyin Abubakar Ladan ne. Ina zuwa har gida na gaishe shi na yi masa alheri, saboda fasaharsa, domin aikin da ya yi ba ƙarami ba ne, don ya tabbatar da tarihinmu na lasar Hausa, ya samu dama ya taskace tarihin shugabannin Afrika, wanda ba za mu samu damar yi ba a yanzu. Don kada abin ya tafi a iska ya zama matasa ba su sani ba. Don haka na ke son ka karanta, ka rera ta yadda ka ke yi, don mu amfana, kuma shi ma za a tuna da shi kuma kai ma albarkar waƙar za ka samu wata daraja kuma mutane za su fa’idantu

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Assalamu alaikum, sakon gaisuwa na ga wannan jajirtacciyar gidan jaridar ta blue print. Haqiqa kun sosa mun inda ya dade yake mun qaiqayi. Ni masoyin marigiyi ne Abubakar ladan Allah ya jaddada rahamarsa agare shi sannan kuma masoyin Aminu ladan ne (Alan waka) dama wakar dana ke ta nema kenan ruwa a jallo. Don Allah menene sunan ita wakar. Nagode ina muku barka da aiki.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan