Majalisar Dokokin Kwara Ta Yi Kira Da A Kwashe Almajirai A Jihar

138

Majalisar Kwara Na Yunƙurin Kwashe Almajirai Daga Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Kwara ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta kwashe almajirai da gajiyyayu daga babban birnin jihar don tabbatar da tsaro.

Majalisar ta yi wannan kira ne a zamanta na ranar Talata.

Felix Awodiji (APC, Irepodun), shi ne ya gabatar da ƙudirin neman hakan, kuma ya samu goyon bayan dukkan ‘yan majalisar

A lokacin da yake karanta ƙudirin, Mista Awodiji ya ce kasancewar almajirai da gajiyyayu a sasaa daban-daban na Ilori babbar barazana ce ga tsaro.

Ɗan majalisar ya bayyana tsoron cewa almajirai da gajiyyayu za su iya zama wakilan mugayen mutane, don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar da kar ta ɗauki kasancewarsu a birnin da wasa.

Wuraren da ake samun almajirirai da gajiyyayun a cewar Mista Awodiji sun haɗa da Oja-Oba, Maraba, Tanke, Sawmill, Geri-Alimi, Ipata Post Office, da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan