Home / Featured / A’a, Shugaba Muhammad Buhari ya na da kyauta – Aliyu Tilde

A’a, Shugaba Muhammad Buhari ya na da kyauta – Aliyu Tilde

(Comment dina da wani ya ce Buhari ya ba wani masoyinsa dubu hamsin bayan ya gayyace shi villa)

Wata rana, a 2002, mun dau jirgi da Buhari zuwa Jos don wata lacca a UNIJOS. Da muka gama muka dawo Haipang Airport, Jos, muna jiran a kammala kimtsa jirgi sai ya ce in miko mar jakar hannunsa. Sai ya bude a tsanake ya ciro bandir din N200 na N20,000 ya ba ni na mika wa ma’aikatan airport din da suka zo gaishe shi. Na mika musu, sai na juya, na ji kwalla sun sabko mun. A zuciyata na ce, “Allah sarki da yana da dukiya mai yawa da ya ba su da yawa—ashe yana kyauta.”

Ita kyauta zuciyar da ta ba da ita ake duba wa ba yawanta ba. Almutanabbi ya ce, “Kad’an daga masoyi, mai yawa ne.”

Ina tunawa mun hadu da shi a Makka ya zo umrah ni kuma na fito Riyadh a 2003. Da jama’a suka watse sai ya dauko wani tarin $100 ya ce, “Ga wannan Dr.” Sai na ce masa, “Ranka ya dade ka fi ni bukatarsu saboda jama’a da kake fama da su a cikin siyasa.” Sai ya ce, “Dr. halinka ke nan. Amma dole ko daya ce ka karba.” Na mika hannu na karba na ce na gode. $100 din nan ta faranta min rai saboda zuciyar da ta bani ita cikin annashuwa da fara’a.

Ina tuna labarin da wani aminina, former VC na UDUS, ya ba ni. A shekarar 1975, yana dalibi, ya je ya ofishin Buhari yana Gomna a Maiduguri don ya nema wa MSS gudunmawa na yin Annual National Conference. Buhari da ya ji daga Zariya suke kuma suka gaya masa abinda ya kawo su, sai ya ce a kai su gidansa su ci abinci sannan a dawo da su.

Da suka dawo sai ya ce musu su yi hakuri babu irin wannan kudin a kason kudin gomnati—watau budget. Amma sai ya dauko N200 tasa ya ce ga gudunmaarsa ta kashin kansa.”

Ina ga mutane da yawa da suka bi Buhari ba su fahimci yadda yake kallon abubuwa ba. Mutum ne mai tsananin fulaku da kara da kamun kai da yin abu daidai karfinsa. Wannan hali nasa har abada yana burge ni kuma abin koyi ne. Bature ma zai ce, to a fault, don har ta kai Buhari ba ya tsawatawa na kasa da shi saboda kara. Da ake ta kuka da na kusa da shi wadanda suka jagoranci CPC, sai ya ce toh ya zai yi da su tunda sune a jinkinsa?

A daya bangaren kuma ba zai ce a baka mukami ko kwangila ba saboda abotarku. Sai dai idan an ba ka a karkashinsa—koda kuwa danginsa ne kai—ba zai ce komi ba. Wannan abinda wadanda suka yi masa hidima a siyasar 2015 ba su gane ba ke nan. Ka masa bisa akida kawai amma ba don ya biya ka ba. Ya ce gyaran mulkin da zai yi shi ne sakayyar duk wanda suka taimaka masa a bisa akida. Da Mbaka ya je wajen wasu kasa da Buhari ne da ya samu biyan bukata fiye da tinkarar Buhari.

Amma don kyauta kam da kara, Buhari yana da su. Kuma abu game da shi wanda na fi so ke nan. K’in sa bakinsa kai tsaye a kwangila da ba da mukami kuwa kare mutuncinsa (integrity) ne wanda tsohon halinsa ne tuntuni. Ko list na mukamai a karkashinsa a matsayin shugaban kasa sai dai su ‘cabal’ ko komiti su tsara amma ba shi ba. Idan mutum bai sani ba sai ya dauka ya mance da shi ne. Wallahi sam. Ya san duk wanda ya yi mar, hairan ko sharran. Kuma ba wai hassada ba ce ko keta ko mugunta ce da shi ba. Ko daya Buhari yi da wannan. Idan ka fahimce shi shi ke nan.

Wajen da kawai na bambanta da shi shi ne kara a guna tana da iyaka musamman ga mai mulki kamar yadda na rubuta a nasihata gare shi a farkon mulkinsa. Wasu yan’nijeriyan wallahi sai da murtuke fuska, da muzurai, da tsawa, da barazana, da takewa da takalmin karfe kafin mulki ya yi karko. Idan ba haka ba, kan ka ce kwabo yan’iska sun mamaye ka sun bata maka mulki. Ina bakin cikin cewa wannan shi ne ya faru a wannan zubin mulkin nasa da bai yi sa’ar makusata ba.

So wanda Buhari ya ba shi N50,000 yana shugaban kasa kar ya dauka rowa ne. Da kudin ya fi haka ma, da irina sun tuhumce shi. Ya yi murna ya kira shi villa, sun gaisa har ya masa kyauta saboda kauna da mutunci. Kar ya duba yawan kudin.

Ita shaidar gaskiya ta zama dole a fade ta a kowane hali.

Dr. Aliyu U. Tilde, shi ne kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Wasiƙa zuwa ga marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua

Bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin dausayin rahamar ubangiji, Allah ya sa haka Amin. …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *