Home / Rayuwa / Banyakole: Garin Da Mahaifiya Ke Kwanciya Da Mijin ‘Yarta

Banyakole: Garin Da Mahaifiya Ke Kwanciya Da Mijin ‘Yarta

Yawanci rawar da ƙanwar mahaifiya ke takawa shi ne nuna soyayya tare da shiryar da ‘yar ‘yar uwarta ta hanyar zama abokiyar sirrinta musamman ta fannin abubuwan da ba za ta iya tattaunawa da mahaifiyarta ba.

Amma a Banyakole, wani gari da yake Uganda, aikin ‘yar uwar mahaifiya ya wuce bada shawara kaɗai.

Ƙabilar Banyakole, waɗanda ake kira ƙabilar Ankole, su ne mazauna Masarautar Bantu Kingdom, wadda take tun ƙarni na 15.

Masarautar wadda take a Kudu Maso Yammacin Uganda, gabas da Tafkin Edward, Sarki Mugabe ne mulketa, kuma ta yi suna saboda bukukuwata na aure da suka sha banban da na saura.

Aure a wannan ƙauye yana da muhimmanci sosai saboda iyaye suna farin ciki da alfahari idan ‘ya’yansu suka yi aure.

A al’adar Banyakole, idan mace ta kai shekara takwas ko tara, aikin ‘yar uwar mahaifiyarta ne ta fara shirya ta kan yadda ake rayuwar aure. Ƙanwar mahaifiyar za ta koya mata duk wani abu da take buƙatar sani na zaman aure a matsayin mace kuma musamman a matsayin matar aure.

Wannan ƙabila tana matuƙar girmama budurci. Hakan ne yasa dole ‘yan mata su ƙaurace wa jima’i kafin aure. Kuma idan aka samu wata budurwa ta san namiji kaifin aure, za ta fuskanci hukuncin kisa ko kuma a ƙaurace mata.

Haka kuma, a wajen ƙabilar Ankole, kasancewar mace siririya ba abin sha’awa ba ne. A wajensu, ƙiba wani abu ne mai jawo hankali wajen jima’i. Saboda haka, idan ‘yan mata suka kai shekara takwas zuwa tara, ana buƙatar su fara ƙoƙarin yin ƙiba ta hanyar tilasta musu cin gero, naman shanu da madara. Yawanci suna yin haka ne don su sa budurwa ta yi ƙiba da wuri don ta iya samun miji.

Auren Banyakole ya ƙunshi bukukuwa da dama da suka haɗa da al’adar bayar da budurwa da suke kira “Kuhingira”, inda dangi da abokan amarya sukan ba ta kyaututtuka kamar ta shanu da sauran kayan abinci don ta tafi da su gidan miji.

Sannan bayan kwana 10 sukan yi wani bikin bauta da suke kira “Okukoza Omunuriro”. A wannan biki, amarya tana kunna wutar farko a sabon ɗakin girkinta.

A ranar ɗaura aure, ana shirya wani bikin a gidan amarya, inda mahaifin amarya zai yanka bajimin sa, a gidan angon kuma, akwai wani bikin shi ma da ake shiryawa don a tabbatar da auren. Amma da farko, akwai wani bikin gargajiya na ƙarshe, wani biki da ya ƙunshi wasu gwaje-gwaje guda biyu waɗanda dole ‘yar uwar mahaifiyar ta yi su.

Tun da budurci shi ne ƙa’idar aure ga ‘yan matan Banyakole, dole ne ‘yar uwar mahaifiya ta gwada budurcin kowace amarya kafin aure. Idan amaryar ta ci gwajin budurcin, za a yi zaton cewa ba ta san mene jima’i ba, kuma ba ta san yadda za ta gamsar da namiji a wajen jima’i ba.

Gwaji na biyu shi ne ‘yar uwar mahaifiyar amarya za ta gwada lafiyar angon ta ɓangaren jima’i, inda za ta yi jima’i da shi.

A lokacin wannan gwaji na jima’i, tana koyon dukkan dabarunsa na jima’i da kuma irin kwanciyar da ya fi so. Bayan haka ne za ta faɗa wa ‘yarta abin da angon yake so a wajen jima’i. Banyakole sun yi imani cewa wannan al’ada za ta taimaka wa amaryar ta gamsar da mijinta a wajen jima’i.

About Hassan Hamza

Check Also

Wani Mutum Ya Kashe Limami Sakamakon Zargin Sa Da Soyayya Da Matarsa

Wani Mutum Ya Kashe Limami Sakamakon Zargin Sa Da Lalata Da MatarsaWani mutum a jihar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *