Home / Labarai / Ƴan Jarida na da ruwa da tsaki wajen bunƙasar Najeriya – Bukola Saraki

Ƴan Jarida na da ruwa da tsaki wajen bunƙasar Najeriya – Bukola Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa ƴan jarida na da rawar takawa wajen bunƙasar cigaban Najeriya.

Sanata Bukola Saraki ya bayyana hakan ne a saƙon sa da ya aikewa da ƴan jaridu a shafin sa na facebook, a cigaba da ranar ƴan jarida ta duniya da ake gabatarwa a ranar 3 ga watan Mayun kowacce shekara.

“‘Yan jarida muhimman masu ruwa da tsaki ne wurin bunƙasar Nijeriya. A zamanin mulkin mallaka na turawa, kafafen watsa labarai ne suka jagoranci rajin da ya samar mana da ƴancin kai. A zamanin mulkin soja ma haka, kafafen watsa labarai ne suka jagoranci yunƙurin da ya ɗora mu bisa tsarin dimokraɗiyya”

Ya ƙara da cewa “Yanzu da muke ta ƙoƙari don inganta dimokraɗiyyarmu, kafafen watsa labarai sune a sahun gaba wurin fafutukar samar da daidaito, adalci, haɗin kai, da cigaban Nijeriya’

“Bisa wannan ne ma, yayin da muke tunawa da ranar ‘yancin ‘yan jarida a yau, nake yin tarayya da sauran shugabanni a faɗin duniya don jinjina ga irin ƙarfin ikon da kafafen watsa labarai suke da shi a rayuwar al’umma”

Haka kuma Sanata Abubakar Bukola Saraki ya ce “wannan rana, ina fatan za mu ci gaba da ƙarfafa kafafen watsa labarai, wanda ɗaya ne cikin ginshiƙan dimokraɗiyya”

A ƙarshe ya ce “Dole ne mu tallafawa ‘yan jaridarmu don su riƙa bayyana labarai masu nauyin da za su taimaka wurin ginuwarmu; su tilasta shugabanni da ma’aikatanmu yin abin da ya dace; samar da zaman lafiya da haɗin kai; tare da shigar da kishi da ƙaunar ƙasa ga zukatan ‘yan ƙasa”

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *