Bayyanar ‘Shehu’: Matakan Kare Kai Daga Korona

189

Bayan ɓullar cutar Korona a duniya har nahiyar Afrika, ciki har da Najeriya, mutane da dama sun shiga neman magunguna da hanyoyin kariya daga ita, sai dai kash! dukkan magungunan da ake ikirarin suna maganin cutar ba sahihai ba ne.

Mutane da dama, musamman a wasu yankuna na Najeriya, na ganin cewar, idan aka yi dace wajen amfani da wasu magunguna na gargajiya za a iya kare kai a matsayin rigakafi ko kuma maganin cutar baki ɗaya.

Waɗannan magunguna da ba a tabbatar da su ba sun haɗar da:

  1. Tafarnuwa

2. Man kadanya

3. Ararrabi

4. Wanka da ruwan dumi da gishiri

5. Citta

6. Albasa

7. Ganyen sabara

8. Shuwaka da sauransu.

Sai dai dukkanin wadannan jerin magungunan da wasu ke ganin za su yi aiki wajen maganin cutar COVID-19, ba su da sahihanci, sakamakon rashin wata shaidar gwaji ko tabbas akan Ingancinsu da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran masana kiwon lafiya suka yi a kansu.

Shehu

Abu ɗaya da ake da sahihancinsa, shi ne masana sun samar da rigakafin cutar COVID-19, tare da samar da matakan kariya.

Har wa yau, Hukumar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta samar da wasu matakan kariya daga cutar Korona, wanda wadannan bayanai za a iya samunsu a manhajar ‘Shehu’.

Hausawa na cewa rigakafi ya fi magani. Don samun bayanai game da rigakafin allurar COVID-19 da ma wasu bayanai da suka shafi cutar, ku shiga ta wannan masigar dake ƙasa ku riƙa samun bayanai daga ‘Shehu‘ cikin harshen Turanci, Hausa da kuma Kanuri.

https://api.whatsapp.com/send/?phone=%2B2347034146757&text&app_absent=0

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan