Home / Addini / Fahimta Fuska: Addinin Musulunci ya amince da ‘Halaccin’ yin shirin Fim – Sheikh Ibrahim Khalil

Fahimta Fuska: Addinin Musulunci ya amince da ‘Halaccin’ yin shirin Fim – Sheikh Ibrahim Khalil

Shugaban majalisar malaman jihar Kano, kuma tsohon mai bai wa gwamna Ganduje shawara a kan ayyukan na musamman, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa addinin Musulunci ya amince da halascin yin shirin wasan kwaikwayo.

Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana haka ne a gurin taron faɗakarwa da kuma shan ruwa da Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa ta MOPPAN rashen jihar Kano, ta shiryawa kafatanin ‘yan ƙungiyar da ke masana’antar Kannywood, a jiya Lahadi.

Taron mai taken Fim a Musulunci, tasirinsa da kuma ƙalubale, wanda malam mai faɗakarwa Ibrahim Khalil ya yi tambihi kan tasirin Fim ga al’umma tare da bayyana wasu daga cikin ƙalu balen da masana’antar ya kamata tashi tsaye domin ganin an kawar da wannan matsalar.

Ibrahim Khalil ta cikin jawabinsa ya bayyana cewa” sana’ar Fim hanyace mafi sauƙi wurin isar da saƙo tare kuma da yin tasiri ta cikin abinda mutane suka kalla a cikinsa, duk da cewar wasu daga cikin malamai sukan soki fim wanda jama’a basu gane ba cewar malamai ba sukar fim ɗin sukeyi ba illa suna sukar abinda aka nuna a cikinsa wanda bai dace ba amma shi fim karan kansa bashi da wani aibu, kuma hakan alhakine ga hukumar tace fina – finai da masu duba Fim kan ya fita ga jama’a, domin samar da abu na gartacce wanda baza’a soke shi ba ko bayyana wani aibunsa”.

Malam ya kuma ƙara da cewa “A lokacin daular Usmaniyya shekara kamar ɗari uku ko huɗu koma biyar da suka shuɗe, anso ayi wani Fim na Annabi Musa Alaihimussalatu Wassalam, wanda wasu yahudawa su ka ce za su yi amma da aka tambayi Daular Usmaniyya sai su ka ce ba za a yi wannan fim ɗin ba, amma daga baya abinda malamai suke kai a yanzu hatta malaman Saudiyya, ta cikin littafinsu ‘Allajinatudda’ima’ wato kwamitin fatawa na din-din-din sun yadda cewa za a iyayin Fim, sai dai sun yi magana akan abu guda biyu idan ‘Annabi Sallallahu alaihi Wasallam’ ake so a yi fim akan sa ko akan wani Annabin da sauran sahabbansa to wannan jarumin ba zai fito fili mutane su ganshi ba kuma yayi actin a matsayin su ba, sai dai ya zamana kamar yadda akayi fim ɗin nan na Annabi Ibrahim wanda sai dai a ji maganar mutum amma suffarsa ba za ta bayyana ba, amma duk wani wanda ba Annabi ba kuma ba sahabi ba to kowanne mutum zai iya fitowa ya yi actin kamar su wannan babu laifi”.

Da yake zayyano irin tasirin fim ga al’umma Malam ya ce ” Fim ko Sinima ba laifi bane a cikin Musulunci, sai dai idan abinda akayi akwai laifi a ciki, su kuma fim wata hanyace ta isar da sako domin akwai hanyoyin tura saƙo uku da muke da su shine ko kaji ko ka gani ko kuma ka karanta, shikuwa fim ya haɗa wannan hanyoyi guda biyu tunda ta haɗa ji da kuma gani, kuma itace hanya mafi saurin isar da saƙo saboda mutum yana ji kuma yana gani, bugu da ƙari akan samu wani ma mai ɗauke da rubutu wato ‘subtitles’ kunga kuwa an haɗa hanyar isar da saƙo guda uku kenan, sannan bazaka hana Fim ba domin baka da wata hanyar isar da saƙo da sauri kamar fim, shiyasa malamai basu taɓa haramta fim ba, sai dai suce abu kaza a cikin fim bai dace ba kuma kai baka zauna kaga fim ɗin harzuwa ƙarshe ba ballantana kayi hukunci, don haka fim yana da tasiri matuƙar gaske ga al’umma wajen canza musu halayya ta hanyar kwai kwayo”.

Sheikh Ibrahim Khalil a gurin taron

Haka kuma Shehin Malamin ya bayyana irin ƙalubalen da ita kanta masana’antar Fim ta shiga musamman Kannywood, ya bayyana cewa ” akwai rashin saka hannun gwamnati a cikin wannan masana’antar, kamar yadda wasu daga cikin gwamnatoci su ke yi na bayar da kuɗi domin a yi shirya Fim kan doka da oda ko wani abu da ya sha ka mutane musamman wasu daga cikin cututtukan da ya kamata mutane su sani da hanyar kariya ta hanyar shirya fim, sannan akwai wani ƙalubale da mu kanmu malamai da muka tashi domin ganin an samar da wani ƙauyen shirya fim wato Film Village da gwamnati taso ginawa amma da su kansu ‘yan Fim ɗin aka yaƙe mu wanda kuma ada mun ɗauki alwashin tsayawa tsayin daka don ganin munkareta daga duk wani tunani da jama’a suke akai, akwai ƙalubalen da haryanzu mawadata basu gane cewar ana samun arziki a cikin masana’antar Fim ba basu san kuma amfanin ta ba, daga cikin kalubalen akwai yadda wasu daga cikin ‘yan Kannywood ke kambama magana ta hanyar rashin jituwa da wasu daga cikin jarumai wanda sukeyi da faɗa wanda kuma da zarar hakan ya faru za a fito aita ya ya ta wa wanda hakan bai kamata ba, kana akwai ɗebo marasa hankali a cikin fim ba wai masu hankali ba wanda kawai da zarar fim ya fito shikenan, ba a zuwa a nemi wanda yake da cikakkiyar sana’a kan abinda fim ɗin ya ƙunsa kan ace anfara fim ɗin domin samun ilimin yadda fim ɗin zai ja hankalin ‘yan kallo”.

Harwa yau Malam ya bayyana cewar akwai buƙa samun ƙwarewa a cikin wannan masana’anta ta Kannywood wanda yanzu ake da ƙaranci.

Jaruamai da damane dai suka halarci wannan taron wanda suka haɗar da mata da maza irin su Ibrahim Mandawari, Auwal Marshal, Hassan Giggs, Kamal S. Alƙali, T.Y Shaban, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Bala Anasa Babinlata, Ali Jita, Salisu Giɗaɗo, Umar Gombe, shu’aibu Lilisko, Isma’i Khalil Ja’in da sauran jarumai maza.

A ɓangarena mata kuwa akwai Hajiya Asma’u Sani, Hauwa A. Bello Editor, Saratu Giɗaɗo Daso, Teema Makamashi, Maryam CTV, Hadiza Kabara, Hadizan Saima, Maijidda Abbas, Ladidi Fagge, Aisaha Abubakar da sauransu.

Andai ci ansha ansada zumunci tahanyar ɗaukar hotuna tare da zama teburi ɗaya wajen cin abinci wanda aka gudanar bayan ankammala jawabin Malam Ibrahim Khalil.

To sai dai an lura da cewa wasu daga cikin manyan jaruman dake Kano basu halarci wannan taro shan ruwan ba, wanda hakan ake dan gantashi da babbancin ra’ayin da ke tsakanain jaruman kan siyasa.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *