Home / Addini / Haramun ne baiwa ƴan bindiga kuɗin fansa – Sheikh Ibrahim Maqari

Haramun ne baiwa ƴan bindiga kuɗin fansa – Sheikh Ibrahim Maqari

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheik Ibrahim Ahmad Maqari ya bayyana cewa addinin musulunci ya haramta baiwa ƴan bindiga kuɗin fansa a lokacin da su ka yi garkuwa da mutane.

Malamin, wanda shi ne kuma limamin babban masallacin Juma’a na Abuja, ya faɗi hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sadarwa na zamani, wanda ya hasko malamin a cikin wani masallaci yana jawabi.

Magana muhimmiya ita ce baiwa masu garkuwa da mutane kuɗi dan a fanshi ɗan adam! Ida har Allah (SWT) zai hana baiwa maƙiya na yaƙi kuɗi dan kar ka karfafesu su cigaba da yaƙar ku, to ina ga mutanen dan Zalunci da Ta’addanci za su zo su kama mutum su ce sai an basu kuɗi an haɗa musu kuɗi sannan za su sake shi, ku haɗa kuɗi ku bayar a sakin wannan mutumin haramun ne laifi ne”

Haka kuma Shehin Malmin ya kafa hujja da Hadisin da wani mutum ya je wurin Manzon Allah yana tambayarsa kan abin da zai yi idan wani ya yi yunkurin ya yi masa fashi da makami, inda Annabi (SAW) ya umarce shi da ya yaƙe shi.

Haka kuma Farfesa Ibrahim Maqari ya ce idan har mutum ne a ƙashin kan sa ya ɗauki kuɗi ya baiwa ƴan fashin dajin domin ya fanshi kan sa to wannan damar sa ce, amma ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci.

Idan a ciki kudinsa ya ga dama shi da kan sa ya cire cikin kudinsa ya fanshi kan sa, to wannan ya ga dama amma ba shi abin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya zabar masa ba” In ji Farfesa Ibrahim Maqari

Hare-haren yan bindiga tare da garkuwa da mutane sun ta’azarra a cikin watan Apirilu a kasar nan, domin a cikin makon da ya gabata kachal, akalla mutane sama 240 aka salwantar da rayuwarsu wasu gwammai kuma aka yi garkuwa dasu.

Tuni dai ƴan adawa da ma ɗaiɗaikun al’ummar kasar nan su ke zargim shugaba Muhammad Buhari da gazawa wajen tabbatar da tsaro a yankunan ƙasar nan, inda aka kiyasta cewa kimanin mutane sama da miliyan biyu ne ke gudun hijira a ƙasashe makwabata bayan hallaka wasu masu ɗimbin yawa.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *