Home / Gwamnati / Ba Za Mu Yadda Da Duk Wani Yunƙurin Juyin Mulki Ba— Rundunar Sojin Najeriya

Ba Za Mu Yadda Da Duk Wani Yunƙurin Juyin Mulki Ba— Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu kira a gare ta domin ta ƙwaci mulki daga hannun gwamnatin farar hula da su guji yin hakan.

Rundunar ta yi gargaɗin ne a wata sanarwa da Mai Magana da Yawunta, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafinsa na Intanet, a cewar BBC Hausa.

Ya ce sojoji ba za su sanya kansu cikin lamarin da zai gurgunta mulkin dimokraɗiyya ba, yana mai ƙarawa da cewa za su murƙushe duk wani yunkuri na kifar da gwamnati.

“An jawo hankalin manyan jam’an soji bisa kalamin da wani da ake kira Robert Clark SAN ya yi, inda yake bayar da shawara cewa jagororin mulkin siyasa su miƙa mulki ga sojoji domin sauya fasalin ƙasar nan. Rundunar sojin Najeriya tana mai tsame kanta daga wannan kalami da ya ci karo da tsarin dimokraɗiyya”, in ji Birgediya Janar Nwachukwu.

Ya ƙara da cewa Rundunar Sojin Najeriya tana “son yin amfani da wannan dama domin ta gargaɗi ‘yan siyasar da ba su da alƙibla waɗanda ke son mulkin ƙasar nan ba ta hanyar zaɓe ba da su guji yin irin wannan tunani” domin a shirye sojoji suke su kare ƙasar.

“Muna son tuna wa dukkan jami’an soji cewa yin tunanin juyin mulki laifi ne na cin amanar ƙasa. Za a hukunta duk wanda aka samu ya haɗa baki wajen aiwatar da irin wannan shiri,” in ji shi.

About Hassan Hamza

Check Also

Ni da Obasanjo mu ka kuɓutar da ɗaliban babbar kwalejin gandun daji ta Afaka – Sheikh Gumi

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *