Home / Siyasa / Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ce wasu ‘yan Najeriya marasa kishin ƙasa na ƙoƙarin haɗa kai da ƙabilu daban-daban da nufin shirya wani taro inda za su kaɗa ƙuri’ar yanke ƙauna ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Kafafen Watsa Labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka ranar Talata a cikin wata sanarwa mai taken: “Martaninnu Ga Saƙon DSS”.

Sanarwar ta ce burin waɗancan mutane shi ne su ƙara jefa Najeriya cikin tashin hankali.

A kwanan nan ne Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta ce akwai wasu mutane da suke ƙoƙarin kifar da gwamnati da kuma ikon Najeriya.

Mista Adesina ya ce wasu shugabannin addini da shugabannin siyasa na baya su ne suke kitsa wannan abu.

Sanarwar ta ce gwamnati mai ci za ta ci gaba da haɗe kan ƙasar nan, duk da kuwa wasu marasa kishin ƙasa ba sa so.

About Hassan Hamza

Check Also

Ni da Obasanjo mu ka kuɓutar da ɗaliban babbar kwalejin gandun daji ta Afaka – Sheikh Gumi

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun …

One comment

  1. Mohammed Abdullahi

    Allah ya yi mana maganin su. Duk mutumin da ke kokarin kawo tashin a wannan ƙasa. Allah ya mayar masa da aniyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *