Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

269

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa Yar’adua ke cika shekaru 11 da rasuwa.
Kafin rasuwarsa, ya sha kai da komowa zuwa kasar Saudi Arabia domin neman lafiya wanda har a wannan lokacin hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.
Haka kuma wani sautin murya da ke yawo a shafukan sadarwa na zamani, da aka jiyo muryar shugaba Yar’adua yana jawabi akan yadda ƴan siyasar Najeriya su ke kitsi maguɗin zaɓe domin samun nasarar kaiwa ga darewa kujerar mulki.


A cikin sautin muryar marigayi Matawallen Katsina Umaru Musa Yar’adua, ya yi jan hankali akan ƴan siyasa da su guji aikata hakan domin zai iya kaiwa ga rushewar dimokuraɗiyyar ita kan ta.

Ga dai abin da marigayi Malam Umaru Musa Yar’aduan ke faɗa:

A lokacin zaɓe na ƙasa mu shuwagabannin siyasa na ƙasar nan da na jihohi in zaɓe yazo kowanne irin zaɓe ne muna fita, maimakon mu fita mu yi yaƙin neman zaɓe na neman ra’ayin jama’a su zo su zaɓi mutanen da muka tsaida a bisa aƙidojin mu ko kuma bisa kyakkyawan halayen mutanen nan na cewa za su riƙe amanar jama’a a ƙasa, to ba ma yin haka nan”

Yawanci yanzu abinda ya ke faruwa wanda kowa ya sani shi ne mu shugabanni sai mu zauna mu shirya ɓarna mummuna, mu shirya shin ranar zaɓe, a rumfar zaɓe kuɗi nawa zamu ba ma’aikatan zaɓe don su shirya rashin gaskiya, mu shirya kuɗi nawa za mu bawa ƴan sanda da jami’an tsaro dake rumfar don idan ana yin rashin gaskiya su kau da kansu, kuma in wani yayi magana ya ce wannan abu ba gaskiya ake yi ba, ya kamata a ce a yi gaskiya, a kama shi a yi masa sharri a kulleshi”

Mu shirya kuɗi nawa zamu bawa masu tsaron akwatu na jam’iyyar da muke hamayya da ita don su ci amanar jam’iyyar su, a yi rashin gaskiya su ci amanar jam’iyyar su tare da su, mu shirya kuɗi nawa za mu bawa manya jami’an tsaro da manyan jami’an hukumar shirya zaɓe”

Na faɗi cewa yanzu wannan abun da ake yi haka yadda ake shirya zaɓe a ƙasar nan wannan shi ne ke ba da mulki ba ashe ba Allah ba? Yanzu wannan abin da ake wannan ɓarnar da ake tafkawa nan ƙasar wurin zaɓe, yanzu wannan ba abin kunya bane ga duk mai hankali a cikin ƙasar nan ta Najeriya? Yanzu wannan ita ce demokraɗiyya ɗin da ake magana? Wannan ba demokraɗiyya ba ce, abinda ke cikin wannan zalunci, ƙarya, cin amana, munafunci da kuma makirci”

Ya ya muke tsammanin mu shugabannin siyasa da ƴan siyasa Dimokuraɗiyyar za ta dawwama a ƙasar nan ana waɗannan ɗanyun ayyuka da mugun aiki?”

Ya ya muke tunanin ita siyasar kanta muna waɗannan abubuwan a ce Allah zai batta a samu dawwammar demokraɗiyya? Su kuma mutanen da su ke binmu suna bin mu ne su tsaya lalle-lalle dole su ce sai wane gani suke suna da wasu buƙatu wanda sai wane ɗin nan ya kai kan bisa kujerar mulki za su yi amfani da shi su sami biyan buƙatunsu”

To wannan hanyar mutane su sani idan Allah ya tashi bawa mutum mulki ko an bi wannan hanyar wadda ba ta da kyau ko ba a bi ba ba ya ta da alƙawarin shi zai bashi mulkin”

Amma waɗannan hanyoyi da ake bi cikin siyasar ƙasar nan, wanda ya samu mulkin sai mulki ya zamo mi shi masifa, wanda suka tisa mutumin gaba suna ta ja za gaba suna ta cewa lalle-lalle sai shi, yana hawa kujerar mulkin da su zai fara ɓatawa, ya zamana ma ganinsu ba ya son yi, don a lokacin ne za su san cewar ba hawan shi kujerar zai biya musu buƙatunsu ba, mai biyan buƙatar daban yake, shi kuma wanda ya hau kan kujerar zai hau ɗin yana bisa da bayan ya sauka abin ya zama masifa gareshi

Takaitaccen Tarihin Umaru ‘Yar Adua

An haifi Malam Umaru Musa ‘Yar Adua ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a garin Katsina.

Mahaifinsa tsohon ministan Legas ne a jamhuriya ta daya kuma matawallen Katsina, sarautar da marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya gada.

Ya shiga makarantar firamari ta Rafukka a shekarar 1958, kuma daga bisani aka mayar da shi makarantar firamari ta kwana da ke Dutsimma.

A shekarar 1965 zuwa 1969 ya yi kwalejin gwamnati ta Keffi.

Daga nan kuma ya tafi kwalejin Barewa, inda ya kammala a shekarar 1971.

Ya shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1972 zuwa 1975, inda ya yi karatun digirinsa na fannin ilimin koyarwa da na kimiyyar sinadirai.

A shekarar 1978 ne ya koma jami’ar Ahmadu Bellon domin yin digirinsa na biyu a fannin ilimin kimiyyar sinadaren.

Aikin farko da Malam Umaru Musa ‘Yar Adua ya fara shi ne na koyarwa a kwalejin Holy Trinity da ke Legas a shekarar 1975 zuwa 1976 kuma daga bisani ya koma koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Zaria a tsakanin shekarun 1976 zuwa 1979 ya kuma ci gaba da koyarwa a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Zariya har zuwa 1983.

Daga nan ya yi aiki a wurare daban daban.

A lokacin jamhuriya ta biyu ‘Yar Adua ya kasance dan jam’iyyar PRP yayin da a wannan lokacin mahaifinsa ne mataimakin shugaban jam’iyyar NPN na dan wani lokaci.

A lokacin da janar Ibrahim Babangida ke shirin maida mulki ga hannun farar hula, Umaru Musa ‘Yar Adua ya kasance daga cikin mutanen da suka kafa wata kungiya mai suna Peoples Front wadda wansa Janar Shehu Musa Yar Adua ya jagoranta, kuma ita ce ta rikide ta zama jam’iyyar SDP.

A shekarar 1991, Malam Umaru Musa ‘Yar Adua ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar SDP inda ya sha kaye a hannun Sa’idu Barda na jam’iyyar NRC.

‘Yar Adua ya sake tsayawa takarar gwamnan jahar Katsina a shekarar 1999 karkashin tutar jam’iyyar PDP, inda ya yi nasara, an kuma sake zabar sa a shekara ta 2003.

Malam Umaru Musa Yar Ada ya kasance gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa, a wani matakin da wasu ke ganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan