Bidiyon Dala: Rashin hujja ne ya tsorata Jaafar Jaafar ya arce – Gwamnatin Kano

250

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani akan ikirarin da mawallafin jaridar nan ta Daily Najeriya, da ake walafata a shafukan intanet wato Jaafar Jaafar ya yi akan cewa barazanar da ake da rayuwarsa ce ta sanya ya arce zuwa ƙasar Burtaniya domin tsira da rayuwarsa da ta iyalinsa.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba ne ya musanta ikirarin a cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce tsoro ne kawai da rashin hujjar da zai kare bidiyon da ya wallafa ne ya sanya shi guduwa daga ƙasar nan, domin lamarin yana gaban kotu kuma da zarar an kammala bincike za a yanke hukunci.

“Na ɗaya dai gaskiya na yi mamaki ƙwarai da gaske, saboda mu nan jihar Kano tun lokacin da mai girma Gwamna ya samu damar wato shugabancin jihar Kano a matsayin sa na gwamna, bamu da tarihin cusgunawa ƴan jarida ko cin zarafin ƴan jarida. Kuma idan ka duba yadda abubuwa su ke tafiya, wannan harka ta maganar bidiyo za ka ga abu ne da ya faru kusan shekara biyu da ta shige”

“Shi Jaafar Jaafar ya kan zo Kano, ba inda ba ya zuwa a jihar Kano, ba wanda ya taɓa cin zarafin sa, ba wanda ya nemi ya cusguna masa ko kuma ya hanashi walawalarsa da sauransu da rayuwarsa”

“Ni ina ganin wato kusan ko in ce ya tsorata ne, yana ganin me yiwuwa ko ba shi da hujjar da zai iya kare abin da ya buga ko kuma shi wannan faifa na bidiyo tun da ya riga ya san cewa mai girma Gwamna ya shigar da ƙara”

“Kuma bayanin da mai girma Gwamna ya yi a wancan lokacin bayanin da ya yi shi ne duk wata hanya da zai bi bisa ga doka da oda domin ya wanke sunansa idan Allah ya yadda zai yi”

”Saboda haka ba magana ce ta a ce za a ɗau wani mataki da zai barazana ga ran shi Jaafar Jaafar, magana ce ta aje kotu a shigar da ƙara kuma na tabbatar da cewa kotu za ta yi bincike kuma daga ƙarshe na tabbatar da cewa kotu za ta yanke hukunci” In ji Malam Muhammad Garba.

Idan za a iya tunawa dai a cikin makon nan ne Jaafar Jaafar ya ce ya bar Najeriya ne saboda ba shi da ƙwarin gwiwar hukumomi za su iya kare rayuwarsa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mawallafin jaridar Daily Najeriya, Jaafar Jaafar

Haka kuma Ja’afar Ja’afar ya ce zai ci gaba da neman mafaka a ƙasar Birtaniya tare da iyalinsa har sai ya samu tabbacin za a kare rauywarsa idan ya koma Najeriya.

A cikin shekrar 2018 ne mawallafin jaridar ta Daily Nigerian ya saki wasu bidiyo da ke zargin cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne yake karɓar damman daloli daga hannun wani ɗan kwangila a matsayin cin hanci.

Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin yana mai cewa ƙirƙirar bidiyon aka yi

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan