Masarautar Kano ta sanar da ranar naɗin Aminu Babba Dan Agundi a matsayin sabon Sarkin Dawaki Babba, kuma ɗaya daga cikin masu zaɓen Sarki a masarautar ta Kano.
Sanarwar na kunshe ne cikin wani gajeren sako mai ɗauke da hoton Basaraken da ke gayyatar ƴan uwa da abokan arziki domin halartar naɗin.


Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2003 ne marigayi mai martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya sauke Aminu Babba Dan Agundi daga mukamin nasa, bayan an zarge shi da nuna rashin da`a ga sarki, da aikata wasu laifuka da suka saɓa da daɓi’un mai riƙe da muƙami irin nasa.
Cikin dabi’un har da korafin da aka ce al`umar masarautarsa ta rubuta a kansa, tana zarginsa da shiga harkar siyasa da shirya magudi, a zaben da aka yi a shekera ta 2003. Amma ya musanta.
A yanzu dai za a yi bikin naɗin na Sarkin Dawaki Babba a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2021 a fadar Kano.