Shirin fim ɗin ISHARA ya fito da hanya mafi sauƙi wajen magance matsalar tsaro a arewacin Najeriya

  3

  Sakamakon matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya musamman a yankin arewacin Najeriya ya sanya ƙungiyar Concern Citizens for Development Initiative ta ɗauki nauyin shirya wani gajeren shirin Fim mai suna ISHARA.

  ISHARA gajeran labarin film ne da ya ke nuni akan muhimmancin miƙa lamari ga Allah a duk lokacin da al’umma su ke fuskantar wani bala’i ko masifa.

  A cikin shirin Fim ɗin an nuna yadda tsananin rashin tsaro tare da masifar hare – haren ƴan bindiga ya tilasta al’ummar wani Ƙauye yin gudun Hijira zuwa wani guri na daban. Sai dai akan hanyar su ta yin gudun Hijirar su ka haɗu da wani Malami mai suna Malam Suwidi (Usaini Sule Koki), inda ya tambaye ɗaya daga cikin matan da ke kan hanyar zuwa wani garin na daban dalilin da ya sa za su ƙauracewa garin su.

  Bayan jin dalili daga bakin Kumbo (Hajara Usman) tare da mai gari (Mansur Kwaram). An nuno al’ummar wannan gari sun taru a ƙofar gidan Mai gari, inda Malam Suwidi ya yi musu nasiha tare da jan hankalinsu akan duk inda mutum ya ke to babu shakka masifa za ta iya samun sa.

  Haka kuma Malamin ya ja hankalin al’ummar da su gyara tsakaninsu da Allah tare da mayar da al’amuran su ga Ubangiji mai girma da ɗaukaka domin samun dacewa tare da warwarewar dukkanin al’amuran da su ka tsananta.

  Bayan sa – in – sa daga mutanen wannan ƙauye tsakaninsu da Malam Suwidi, a ƙarshe sun amince tare da karɓar nasihar Malamin, inda aka hasko su a cikin Masallaci suna yin Sallah tare da yin addu’a akan matsalar tsaro da ta addabi al’umma.

  Allah ma ji rokon bawansa domin kwana ɗaya da yin wannan addu’a aka samu rashin fahimtar tsakanin gungun ƴan fashin dajin, inda hakan ya kai su ga hallaka junansu.

  Darasin Shirin Fim Ɗin Ishara

  Tabbas babban darasin da ke cikin wannan shirin Fim shi ne tunasarwa ita ta ke dawowa da mutane hankalinsu jikinsu, idan masifa ta taso musu su nemi taimakon Allah.

  Haka kuma wannan shirin yana ƙara jan hankalin al’umma da su fawwalawa Ubangiji dukkanin wani al’amari tare kuma da yin tuba na gaskiya.

  Karɓar gaskiya a lokacin tsananin ko ƙuncin wata masifa, domin idan hankali ya ɓata to tabbas hankali ne ke dawo da shi.

  Haka kuma shirin Fim ɗin yana ƙara koyar da haɗin kai tare da amfaninsa a tsakanin al’umma. Sai kuma muhimmanci da tasirin addu’a a lokacin tsanani da sauki, domin shi Allah ma ji roƙon bawan sa ne.

  Al’umma Na Da Rawar Takawa

  Dole mutane a koma ga Allah domin tuba da neman kawo karshen wannan dambarwa da ta ki ci ta ki cinye wa.

  A guji tsinewa shugabanni, maimakon haka a rika taya su da addu’a.

  Al’umma ta guji raina abubuwan da ke faruwa domin tashe kafafen barna da ka iya kunno kai

  Su Waye Su Ka Taka Rawa A Cikin Shirin?

  Fitattun jaruman masana’antar Kanywood irin su Husaini Sule Koki da Hajara Usman da Sulaiman Yahaya Bosho da Sharu Mustapha Naburuska. Sauran su ne Jamila Umar Nagudu da Hadiza Mohd Sani da Aminu Ari Babads Mansoor Kwaram da Yusif Baban Chinedu da Tsalha Dandano da kuma Dan’azumi Baba Chediyar Ƴan Gurasa (Kamaye).

  Haƙiƙa wannan gajeren shirin Fim na ISHARA ya yi matuƙar isar da saƙo tare da bayar da darussa masu yawa, kuma tabbas saƙon zai ƙara taimakawa wajen canzawa al’umma tunani akan matsalar tsaro da ake fama da ita a sassan Arewacin Najeriya

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan