Yadda tashin farashin siminta ya janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya

128

Al’umma a Najeriya na fuskantar matsalar hauhawan farashin siminti, lamarin da masu lura da al’amura suke ce yana haifar da tarnaki ga fannin masu gine-gine a kasar nan.

A watan da ya gabata, ƴan majalisar dokokin kasar nan su ka bayyana cewa, mamaye harkar sayar da siminti da wasu kamfanoni uku suka yi, na ci gaba da haddasa tashin farashin mahadin na gine-gine.

A cewarsu, hakan yana haifar da tarnaki a kokarin da ake yi na farfado da tattalin arzikin ƙasar nan wacce ta fi arziki a nahiyar Afirka.

Kashi uku na adadnin mutanen da suka isa yin aiki a Najeriya ba su da abin yi, kuma kasar ta farfado daga komadar tattalin arzikinta ne na biyu cikin shekara hudu a bara.

Kamfanin Dangote na da kashi 60.6 wanda mallakar Aliko Dangote ne, mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka.

Sai Lafarge da ke da kashi 21.8 yayin da BUA ke da kashi 17.6

Mamaye harkar sayar da siminti da kamfanonin suka yi, na tattare ne da haramcin shigar da simintin da aka saka a kasar tun shekara 20 da suka gabata, a wani mataki na sa Najeriya zama mai dogaro da kanta a fannin hada siminti.

Kamfanonin simintina sun kara farashinsu a lokacin da Najeriya ta fuskanci komadar tattalin arziki a shekarar 2016 a wani mataki da suka dauka na rufe gibin rashin ciniki da ba sa yi, kuma tun daga lokacin, farashin ya ci gaba da hauhawa. Baya ga haka, akwai korafi da suke yi na tsadar ayyukan hada simintin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan