Najeriya: Za A Ɗaure Duk Wanda Ya Biya Kuɗin Fansa Tsawon Shekara 15

131

Za A Ɗaure Duk Wanda Ya Biya Kuɗin Fansa Tsawon Shekara 15
Majalisar Dattawa a Najeriya na son a haramta biya da karɓar kuɗin fansa da niyyar kuɓutar da duk wani da aka yi garkuwa da shi, a cewar wani rahoton BBC Hausa.

Haka kuma majalisar ta nemi a yanke wa duk wanda aka kama ya biya ko ya karɓi kuɗin fansa hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari.

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da ƙudirin na 2021 mai taken ‘Magance Ayyukan Ta’addanci”.
Tuni dai ƙudirin ya tsallake karatu na biyu.

Da yake jagorantar muhawara kan ƙudirin, ɗan majalisar ya ce, “dokar ta’addanci ta 2013 tana buƙatar gyara don haramta biyan kuɗin fansa ga masu satar mutane domin sakin duk wani wanda aka sace ko tsare shi bisa kuskure”.

A cewar Onyewuchi, ƙudirin dokar na neman maye gurbin sashi na 14 na Babbar Dokar a matsayin wani sabon sashi kamar haka: “Duk wanda ya tura kuɗaɗe, ya biya ko kuma ya haɗa baki da wani mai satar mutane ko kuma ɗan ta’adda don karɓar kuɗin fansa da niyyar don sakin wani wanda aka sace ko aka tsare ko ɗaure shi to ya aikata babban laifi kuma zai iya ɗaukar hukuncin ɗaurin shekaru 15. “

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan