Makashin Maza: Yadda Gogarman ƴan Boko Haram Abubakar Shekau ya cimma sa’i

156

A safiyar yau Alhamis ƴan Najeriya su ka tashi da labarin rasuwar jagoran ƙungiyar ƴan tayar da ƙayar baya wato Abu Mohammed Abubakar bin Mohammad al-Sheikawi, wanda aka fi sani da Abubakar Shekau.

Abubakar Shekau mutum ne da ke da kaifin kishin addini kuma shi ne jagoran kungiyar nan ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Najeriya da ƙasashe maƙota.

Gabannin kasancewarsa shugaban Boko Haram, Shekau ya taɓa zama mataimakin shugaban kungiyar lokacin da Muhammad Yusuf ke jagorantarta.

Abubakar Shekau ya na daya daga cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo a duniya saboda aikata laifin ta’addanci.

Duk da cewa rundunar sojin Najeriya ta sha fadin cewa ta kashe Shekau ko kuma ta kama shi, inda yake fitowa a bidiyo ya karyata ikrarin sojojin. A wasu lokutan ma rundunar sojin ta sha nunawa manema labarai makaman da ta ce ta kwace daga mayakan Boko Haram har ma da tutocinsu.

Sai dai a wanan karon Shekau ɗin ya cimma lokaci domin sanannen ɗan jaridar nan mai wallafa rahotanni akan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP, kuma babban editan jaridar HumAngel wato Ahmad Salkida ne ya bayyana cewa Abubakar Shekau da kansa ya kashe kansa.

A cikin wani rubutu da yayi a shafinsa na Twitter, Ahmad Salkida ya ce sakamakon arangamar da aka yi tsakanin Shekau da kuma ƙungiyar ISWAP, ya sanya shi miƙa wuya.

A cewar Ahmad Salkida, bayan da ƙungiyar ta ISWAP ta buƙaci Abubakar Shekau da yayi mata mubayi’a ya mika jagoranci gareta, sai yaƙi amincewa da hakan kuma ya tarwatsa kansa da Bom.

A cikin shekarar 2020 sai da Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Amurka ta yi tayin cewa za ta ba da tukuicin dala miliyon bakwai kwatankwacin sama da naira biliyan biyu da rabi ga wanda ya ba da bayanin da zai taimaka wajen kama shugaban kungiyar Boko Haram Abubukar Shekau.

Haka kuma a cikin shekarar 2018 ne rundunar sojin Najeriya ta ce za ta bayar da takuicin dala $8,000 ga duk wanda ya ba ta bayanai da za su kai ga kamo jagoran kungiyar ta Boko Haram.

A yau dai hanya ta shige da Abubakar Shekau cikin ɗaki, domin kamar yadda ƴan magana kan ce Makashin ‘Maza; Maza Kan Kar Shi’, sai dai gogarman Boko Haram din ya mutu ya bar al’ummar Najeriya da ma duk wanda ya karanta tarihin ayyukan ta’addancin da ƙungiyar Boko Haram ta yi karkashin jagorancin sa zai kasance cikin alihini tare da jimami. Haƙiƙa babu shakka al’umma za su yi Allah wadai da Tofin Ala – Tsine ga irin baƙin tarihin da ya bari doron ƙasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan