Gidauniyar Ilimi ta Kwankwasiyya za ta ɗauki nauyin ɗalibai fiye da 100 a faɗin Najeriya

253

Gidauniyar tallafawa Ilimi ta Kwankwasiyya ta bayyana ƙudurinta na ɗaukar nauyin ɗalibai guda huɗu (4) daga kowacce jiha da ke faɗin Najeriya, domin yin karatu kyauta a sabuwar jami’ar Mewar da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaban Gidauniyar Kwankwasiyya, Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ne ya bayyana hakan ta bakin Saifullahi Hassan wanda shi ne mai tallafa masa na musamman a harkokin yaɗa labarai.

Gidauniyar Cigaban Ilimi ta Kwankwasiyya dai ta daɗe tana tallafawa matasa wajen cigaba da karatunsu zuwa kasar India da kuma sauran jami’o’in da ke gida Najeriya.

Wasu daga cikin ɗaliban da gidauniyar tallafawa Ilimi ta Kwankwasiyya ke nan a lokacin da za su tafi ƙasar Indiya karatu

Jami’ar Mewar da ke yankin Masaka a birnin tarayya Abuja ita ce jami’a ta farko a nahiyar Afirka wacce tushenta ke birnin Rajasthan da ke ƙasar Indiya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan