Ranar hawa keke ta duniya: Alfanun da ke tattare da Keke ga rayuwar ɗan adam

13

Hawan keke na cikin nau’oin motsa jiki kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ware uku ga watan Yuni a matsayin ranar bunkasa dabi’ar hawa keke.

A shekarar 2018 Majalisar Dinkin Duniya ta ware rana ta musamman (uku ga watan Yunin kowacce shekara) domin bikin ranar masu hawa keke ta duniya domin tulawar abubuwan da suke shafar hawan keke a sassa dabam-dabam na duniya.

Yayin da ake bikin ranar masu hawa keke ta duniya a wannan wata na Yuni fatan masu kare muhalli shi ne jama’a su fifita hawa kekuna a maimakon motoci da babura wadanda a ilmance ke barazana ga mutum da duniyarsa.

Tuka keke na ƴan wasu mintuna a ranakun mako ko ranaku biyar yana da fa’idoji da dama. Ga kadan daga cikin wadanda na zakulo:

  1. Kiyaye ciwon zuciya: kungiyar likitoci ta Birtaniya wato British Medical Association ta gudanar da wani bincike a kan wasu ma’aikata su 10,000, rabi aka ba,su keke, rabi suka rika hawa mota zuwa aiki na wani tsawon lokaci. Sakamakon ya nuna wadanda suka samu cutukan zuciya a masu hawa mota sun nunka na keke ribi biyu.
  2. Mutum zai dawo saurayi: Masu binciken lafiya a Jami’ar Stanford ta Amurka sun tabbatar cewa masu hawa keke na nishadi, ba na wahala ba, ba sa saurin tsufa. Wannan ana iya samu a kowane irin motsa jiki, amma na hawa keke ya fi.
  3. Barci mai dadi: Samun barci mai dadi ga ma’aikatan ofis yakan yi karanci. Idan ma’aikaci yana hawa keke a kullum, ba shi ba juye-juye.
  4. karfin Cinya da kugu: Inda keke ya fi sauran hanyoyin motsa jiki ke nan. Da yake aikin tukin ya fi yawa a cinya da kugu, duk namomin wannan bangare za su yi karfi, su rage kasala.
  5. Rage Tebar ciki: Tuka keke ya fi sauran hanyoyin motsa jiki sa rage tebar ciki, don aikin a wadannan wurare yake.
  6. Rage Taurin bayan gida: Tuka keke ya fi sauran hanyoyin motsa jiki motsa ’ya’yan hanji, ta yadda ba ruwan mai hawansa da yawan samun taurin bayan gida.
  7. Ga masu ciwon asma ko wani ciwon numfashi: An tabbatar cewa tuka keke ya fi guje-guje alfanu ga masu irin wannan matsala wajen bude hanyoyin numfashi.
  8. Zuwa aiki kan kari: A wasu manyan garuruwa, inda cinkoson motoci kan sa mutane bata mintuna kusan talatin a danja, mai keke ko babur ba ruwansa. Amma babur ma a wasu garuruwan yanzu ya fara zama jidali, turi ko’ina.
  9. Maganin kuiyar motsa jiki: Da dama mutane na son motsa jiki, amma saboda kiuya ba sa yi. Keke na kashe kiuya domin yana sa motsa jiki cikin nishadi, idan mutum ya maishe shi abin zuwa aiki.
  10. Rage dumamar yanayi: Duk yadda aka samu raguwar babura da motoci, ko da kaso kadan ne, to hayakin da ke bata mana muhalli ta hanyar gurbata iskar sararin samaniya, zai ragu sosai. A wasu lokuta, a manyan birane, idan akwai taron abin hawa a danja, idan ka ga hayaki kai ka ce hazo ne ya sauka.

Sai dai da yake yanzu mutane da dama sun riga sun yi kibar da wasu kekunan ma ba za su dauke su ba, yana da kyau ko irin na wuri-daya mutum ya saya a gida ya rika tukawa, saboda ya samu fa’idojin da akan samu, idan ya sabe, ya nemi na yawo. Sai dai fa’idojin wannan ba za su kai na keke mai yawo ba. Mata ma a cikin gidaje za su iya amfani da irin wannan. Wadanda ma ba sa son wannan shawara za su iya sayen na hawa a ranakun da ba aiki.

Wani abu da zai hana mu hawa keke shi ne na jin kunya, saboda a al’adarmu an saba ganinka a mota, amma a zo kuma a ganka a keke. Idan masu mota suka fara a daidaikunsu, abu ya baza gari, zai zo ya zama yayi, a manta da kunya, tunda kowa dai ya san suna da motar. Idan kuma mutum yana da ciwon zuciya, to babu shi a wannan motsa jikin, amma mai hawan jini, zai iya yi. Mai ciwon zuciya ya tuntubi likitansa domin ya san irin motsa jikin da ya kamace shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan