Kar Ku Razana: Yanayi 4 Da Zaku iya Fuskanta Bayan Karbar Rigakafin COVID-19

116
Wani yana karbar Allurar rigakafi

Rigakafin allurar Korona na da matukar tasiri ga garkuwar jikin mutum a yayin da aka masa.

Hakan zai iya taimaka wa garkuwar jiki wajen yaki da cutar Korona da ma wasu cututtuka na daban da ka iya addabar gangar jiki dan Adam.


Wadannan na daga cikin irin yanayin da mutum ka iya fuskanta bayan karbar rigakafin allurar COVID-19:

1. Zafi yayin allurar: a yayin da ake yi wa mutum allurar rigakafin, zai iya jin zafi, amma hakan ba yana nufin wani abu ya faru ba. Kowa zai iya jin zafi yayin da ake masa allura.

2. Gajiya: bayan karbar allurar rigakafin, mutum zai iya fuskantar yanayi na gajiya, hakan zai iya gushewa cikin ‘yan kwanaki.

3. Ciwon kai: wasu na iya fuskantar yanayi na ciwon kai da zarar sun karbi rigakafin, amma likitoci da masana kiwon lafiya sun bayyana cewa ba kowane mutum ne zai fuskanci hakan ba, ya danganta da yanayin hallitar jikin dan Adam, shi ma zai daina cikin wasu awanni ko kwanaki.

4. Zazzabi: akwai yiwuwar mutum ya ji yanayin zazzabi ya kama shi bayan karbar rigakafin allurar Korona. Shi ma zai gushe bayan wasu awanni ko kwanaki.

Dukkan wadannan yanayi da mutum kan iya fuskanta bayan karbar rigakafin allurar COVID-19, suna taimaka wa gangar jiki dan Adam ne wasu fara aiki tare da kafa makarai da za su yaki cutar Coronavirus, sannan su yi kokarin hana ta shiga jikin wanda bai kamu ba.

Tuntubi manhajar ‘Shehu’ don samun karin bayani:


https://bit.ly/3b3Kbnc

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan