Ganduje Zai Mayar Da Ma’aikatan Kano Malaman Makaranta

65

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta umarci Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano ya tura ma’aikata kimanin 5000 masu shaidar aikin malanta zuwa makarantu.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Kano.

Ya ce wannan umarnin ya biyo bayan shawara da wani Kwamitin Ƙwararru da aka kafa don ya duba matsalar shirin ilimi kyauta na gwamnatin Kano.

Kwamishinan ya ce kwamitin ya gano akwai ma’aikata 575 masu shaidar koyarwa a Ma’aikatu, Sashe-Sashe da Hukumomi, MDAs, yayin da ma’aikata 3,712 suke aiki a ƙananan hukumomi, kuma ayyukan nasu sun yi kama da na juna.

Mista Garba ya ce daga cikin wannan adadi, 19 suna da digirin digirgir, 55 suna da digiri na biyu, 1,100 suna da digirin farko na koyarwa, 2,366 kuma suna da Shaidar Koyarwa ta Ƙasa, NCE, guda 10 kuma suna da difloma.

A cewarsa, ofisoshin shiyya da ƙananan hukumomi su suke da tarin ma’aikata da yawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan