A Yammacin yau Alhamis tsohon mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari akan harkokin majalisa, Suleiman Abdulrahman Kawu Sule ya tafi ƙasar Egypt neman magani.
Sanarwar na ƙunshe a cikin wata wallafa da Yasir Ramadan Gwale, wanda makusanci ne ga Kawun, ya yi a shafinsa na facebook yana mai yi masa addu’ar neman lafiya tare da dawowa lafiya.
“Hon Kawu Sumaila na kan hanyarsa ta zuwa kasar Masar domin ganin likita tare da cigaba da duba lafiyarsa. Allah yasa ayi lafiya a dawo lafiya” In ji Yasir Ramadan Gwale.

Wannan dai yana zuwa ne kwana ɗaya da masarautar Rano za ta naɗa Kawun a matsayin Marafan Rano.
Turawa Abokai
Allah ubangiji yabawa kawunmu lafiya