Romon Dimukaraɗiyya: Jerin manyan ayyuka 10 da shugaba Buhari ya yiwa jihar Kano

  285

  Sati guda da ya gabata, shugaban kasa Muhammad Buhari ya hau jirgi, ya tafi Lagos, aka yi kasaitaccen biki don bude katafariyar tashar jirgin kasa, wacce za a rika jigila tsakanin jihar Lagos da jihar Oyo. Wato jirgin kasa zai taso daga tashar Ikorodu a Lagos, ya biyo jihar Ogun sannan ya tuke a Ibadan jihar Oyo.

  Wannan aiki ne muhimmi, ba shakka zai tallafawa kasuwanci da sufuri da cinikayya, kuma zai kara habaka tattalin arziki na Lagos da Ogun da Oyo. Daga nesa ma, zai taimaki sauran jihohin Najeriya.

  Wanda duk ya bi tarihin wannan aikin zai ga ba a satin jiya aka fare shi ba. Tsohon gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode da sahalewar shugaban kasa Muhammad Buhari da kai-komon ministan sufuri Rotimi Amechi da saka idanun Mataimakin shugaba kasa Farfesa Yemi Osinbajo da kulle-kullen National Leader Bola Ahmed Tinubu da uwa-uba jimirin gwamna mai ci na Lagos Sanya Olu aka tsara shi.

  Bayan bude aikin da PMB ya je ya yi, sai budewar kuma ya tada kura, mutanen Kano da sauran mutanen arewa kowa na tofa albarkacin bakinsa.

  Na kalli abubuwa da yawa, sai naga dacewar ina ya kamata mu maida hankali, a maimakon wannan korafin. Gwamnatinmu ta APC ta cika shekara shida akan mulki. Saura shekara biyu PMB ya koma Kaduna ko Daura. Nan da shekara daya, za a buga gangar siyasar shekarar 2023. A cikin ayyukan da gwamnatin Buhari take yi a Kano ko wadanda suka shafi Kano, wasunsu an saka harsashi, a wasu wuraren an fara gini, wasu an kaddamar, wasu suna matakin neman izinin farawa daga bangarori da hukumomi masu yawa.

  A dan abin da na tattara na bayani na samu Capital Projects wato manyan ayyuka guda goma na PMB a Kano da ‘yan uwanta. Na farko, an yi nisa a aikin sabon fasalin Filin tashi da saukar jirgin sama na Mallam Aminu Kano. Tun shekarar 2013 aka fara aikin, an kashe kudi kusan naira biliyan 24. Na biyu ana kan ginin sabon gidan fursuna wato Correctional Center. Wannan aikin zai ci kudi naira biliyan 14. Na uku an ci gaba da aikin titin da ya tashi daga Kano zuwa Wudil zuwa Gaya zuwa Azare har Maiduguri, tsawonsa kilomita 560. Tun zamanin Obasanjo aka fara shi akan kudi naira biliyan 56. Aiki na hudu shi ne yin falle biyu na titi daga Kano har zuwa Katsina birnin Dikko. Titin tsawonsa kilomita 157, shima tun lokacin Goodluck Jonathan aka bada aikinsa. An yi nisa sosai a wannan gwamnatin. Na biyar shi ne aikin titin mota daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya, sannan ya dangana da Kano. Ana kashe kudi kusan naira biliyan 730.

  Haka kuma akwai aiki na shida, an zana taswirar aikin layin dogo kuma an bada kwangilarsa ga kamfanin CCECC. Wannan titin jirgin kasa zai taso daga Kano-Dambatta-Kazaure-Daura-Katsina-Jibiya-Maradi. Zai ci kudi kusan dala biliyan biyu. Aiki na bakwai shi ne yin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Dutse ta Jigawa. Wannan aiki dan uwan dayan ne. Aiki na takwas shi ne aikin da NNPC suka bayar na shimfida bututun iskar gas daga Ajaokuta ya taho Kaduna ya iso Kano. Aiki na tara shi ne yin titi daga Rimin Gado ya wuce Kabo ya tafi Gwarzo ya tsaya a Dayi. Tsawonsa kilomita 83 kuma za a kashe kudi kusan naira biliyan 67. Aiki na goma shi ne babban titin jirgin kasa na Lagos-Ibadan-Abuja-Abuja-Kano. Ana maganar za a kashe dala kusan biliyan biyar, kasar China ake tsammanin su bada rancen kudin aikin kuma su aiwatar da shi.

  Wannan lissafin nawa sam ban yi la’akari da ayyukan da ma’aikatu da hukumomi na gwamnatin tarayya wato MDA’s suke yi na yau da kullum ba. Ban saka ayyukan ‘yan majalisar kasa ba na Constituency Projects, na dauki manyan ayyukan da suka shafi siyasar kasa da dangataka da Kano da sauran sassan tarayya.

  Hankalina ya tafi akan ba shakka Buhari yana ayyuka a Kano, tambayar ita ce shin ayyukan nan za a gama su irin yadda aka yi wa tashar jirgin kasa ta Lagos zuwa Ibadan, Buhari ya zo ya kaddamar da su a ci gaba da cin moriyarsu? Shin manyan ayyukan titinuna sune kadai bukatar da mutanen Kano suke da ita daga gwamnatin tarayya a matsayin Kano cibiyar kasuwanci ta arewa, babbar kasuwa ta Africa?

  Wannan kashin farko ne. Insha Allahu a biyo ni kashi biyu.

  Bello Muhammad Sharada, ya rubuto daga Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan