Masu tsaron baya da suka fi kowa a duniyar ƙwallon ƙafa

354

A tarihin ƙwallon ƙafa anyi masu tsaron baya wanda tarihi ba zai kammala ba, ba tare da ambaton sunayensu ba.

Amma sai dai a yanzu, wasu ma’abota kallon ƙwallon ƙafa su na ganin cewa indai iya tsaron baya ne, to a barwa Sergio Ramos saboda irin ƙwarewarsa da kuma irin salon da yake taka leda.

Sergio Ramos

Sai dai a ra’ayin Mubarak Abubakar, ma’abocin sharhin Ƙwallon ƙafa a dandalin sada zumunta na Facebook, ya na ganin ko kusa Ramos baya daga cikin masu tsaron baya da suka fi iya bada kariya. Mr. Mubarak ya wallafa hakan a shafinsa ma facebook inda yake cewa:

Mubarak Abubakar

“Duk wani article, award ko analysis da zaka duba na ball, na tarihin ball da masana kurra suka tabbatar, kowa ya yarda babu kamar Maldini, Baresi, Beckenbauer a iya defending tunda aka qirqiri ball. Wadannan sune masu masu daraja ta daya da ba’a taba ganin yan baya kamarsu ba a tarihi ta kowace fuska a zunzurutun iya tare. In football, ”Defense is one of the hardest skills to master. While strikers can miss plethora of chances, defenders simply cannot put a foot wrong”!

Maldini daga gefen hagu, Beckenbuaer, Baresi


Bayan su sai irin su Cafu, Bobby Moore, Frank Rjikaard, Facchetti, Cesare Maldini, Pasarella, Gentile, Nesta, Krol, Costacurta masu daraja ta biyu.

Frank Rjikaard daga hagu, Nesta, Costacurta

Sai kuma su Ramos, Lucio, Carragher, Thuram, Puyol, Thiago Silva, Pique, Cannavaro, Carlos, Alves, Terry, Stam, Lahm, masu daraja ta uku. Ina qalubalantar masu cewa Ramos ne G.O.A.T na defenders in history da su kawo link daya,ko wani official FIFA ranking,ko sanannen pundit,analyst,football historian da ya tabbatar da iqirarinsu!”

Ramos, Silva, Puyol, Cannavaro

‘Yan ball attackers nawa Ramos yayi facing wanda duk duniya ta shaida mayu ne kuma with techical abilities to play in the previous star studded era of 80s and 90s? Messi ne kawai zasu iya shiga wancan category din sai su Suarez da C. Ronaldo. Gayamun a cikin su wanda Ramos ya iya shutting down completely in grandest stages and won the game by that!

Alaji ana magana su Baresi,Franz, Maldini, da suka yi ball da arnan attakers sukayi shutting down din su Maradona, Baggio, Van Basten, Platini, Del Piero, Rossi, Romario, Rivaldo, Ronaldo, Gerd Muller wa yake maganar masu cin zalin Salah? Duk wani atracker mai ball a qafa ko qarfi a jiki, ragargaza Ramos yake. Ramos is good no doubt, but cin amanar ball ne a kira shi G.O.A.T of defenders.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan