Matashi A Kano Ya Kashe Kansa Sakamakon Gaza Biyan Kuɗin Jarrabawa

3

Wani matashi a jihar Kano ya kashe kansa ta hanyar banka wa kansa wuta sakamakon gaza biyan kuɗin Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare, SSCE, da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Najeriya, NECO take shiryawa.

Wannan al’amari ya faru ne Talatar da ta gabata a ƙauyen Garo dake ƙaramar hukumar Kabo a jihar ta Kano.

A cewar rahotanni, matashin, mai suna Ɗanladi Shu’aib, ya yi SSCE har sau uku amma yana faɗuwa.

Sai dai a wannan shekarar ya gaza biyan kuɗin jarrabawar.

Wani mazaunin Garo, Ya’u Ahmad Garo, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa marigayi Ɗanladi ya sha cewa zai kashe kansa idan ya fadi jarrabawar.

Ya’u ya ce bayan Ɗanladi ya ƙona kan nasa an garzaya da shi zuwa asibiti, bayan kwana biyu sai rai ya yi halinsa.

Wani maƙobcin mamacin wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce: “Ɗanladi ya je aiki a wani gareji, bayan an biya shi kuɗin aikinsa na ranar, sai ya je ya siyo fetur, ya shiga wani ɗaki, ya zuba fetur ɗin a jikinsa sannan ya banka wa kansa wuta.

“Lokacin da zafin wutar ya ratsa jikinsa sai ya fara kuka yana neman taimako. Mutane suka kashe wutar suka garzaya da shi zuwa asibiti.

“Amma bayan kwana biyu sai ya rasu sakamakon raunukan da ya ji”, in ji majiyar.

Rahotanni suka ƙara da cewa Ɗanladi ya tara rabin kuɗin jarrabawar, amma sai ya fidda rai a lokacin da ya gaza samun cikon kuɗin.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan