Ɗaliban Abduljabbar Sun Sa Ya Nemi Afuwa Game Da Kalamansa

33

Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwa tare da janye kalamansa game da Annabi Muhammadu SAW.

Abduljabbar ya bayyana haka ne a cikin wani saƙon murya da ya aike wa BBC Hausa ranar Lahadi, yana mai fatan: “Hakan ya zama silar gafara da rahama da jin ƙai gare ni”.

“Waɗannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma’aiki SAW, na janye su na kuma janye su.”

Wannan na zuwa ne ‘yan awanni bayan sautin farko da ya fitar a Lahadin yana neman afuwar waɗanda suka fahimci cewa shi ne ya ƙiƙiiri kalaman ɓatanci ga Annabi da ake zargin sa da yi.

 Sheikh-Abduljabbar-Nasiru-Kabara
Sheikh-Abduljabbar-Nasiru-Kabara

A cikin saƙon na farko ya ce: “Idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirar su na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba”.

“Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al’umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su.”
Abduljabbar ya nemi afuwar ne bayan wasu ɗalibansa sun nemi ya yi hakan.

A ranar Asabar ne gwamnatin Kano ta shirya muƙabala tsakanin Abduljabbar da malaman jihar bayan an daɗe ana jan ƙafa game da muƙabalar.

Sai dai malamin ya ce bai gamsu da ita ba, yana mai cewa “ni ba zan kira ta muƙabala ba saboda ba a faɗa mani tsarin ba kafin na zo wurin”, sannan ya ce ba a ba shi isasshen lokaci ba.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Allah me iko… yana kyau malamanmu suke bincike sosai kafin su tara masu binsu su gayamasu abun da bashi ne a addini ba. Allah yasa mudace.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan