Abduljabbar Bai Cika Sharaɗan Tuba Ba – Ganduje

232
Sheikh-Abduljabbar-Nasiru-Kabara
Sheikh-Abduljabbar-Nasiru-Kabara

Gwamnatin jihar Kano ta ce Abdulljabbar Nasiru Kabara bai nemi afuwa ba game da kalaman ɓatanci da ya yi ga Annabi Muhammad S.A.W da sahabbansa.

Kwamishinan Harkokin Addinai na Kano, Muhammad Tahar Adam wanda aka fi sani da Baba Impossible ne ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Litinin.

Kwamishinan ya ce Abduljabbar bai cika sharaɗan tuba da Musulunci ya gindaya ba.

“A Musulunci, akwai sharaɗan tuba guda uku.

“Amma shi bai yadda cewa ya aikata zunubi ba”, in ji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa babu tuba ga duk wanda ya ci zarafin Mala’ikin Allah saboda babu wanda yake da ikon ya yafe masa.

A cewarsa, ma’aikatarsa za ta miƙa wa Gwamnan Kano rahoto game da muhawarar da aka yi da Abduljabbar.

Ya ce Gwamna ne zai yanke hukunci game da matakin da ya fi kyau a ɗauka.

Ya gargaɗi mutane kada su ɗauki doka a hannunsu domin kuwa gwamnati za ta hukunta waɗanda suka yi haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan