Abdulmumin Jibrin ya ɗauki nauyi ɗalibai 2000 domin su rubuta jarabawar NECO da NBAIS
Tsohon ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji zauren majalisar dokokin Najeriya, Honourable Abdulmumin Jibrin Kofa ya biyawa yara dubu biyu (2,000) waɗanda ba za su iya biyan kuɗin jarabawar NECO da NBAIS ta shekarar 2021 Naira 11,500 kowannen su domin su rubuta jarabawar.
A yayin da yake jawabi ga ɗaliban a garinsa da ke garin Kofa a yankin ƙaramar hukumar Bebeji Hon. Jibrin ya bayyana cewa ya biyawa ɗaliban kuɗin jarabawar ne a matsayin gudummawar sa ga ɓangaren ilimi wanda ya na da matukar alfanu a bangarori da dama musamman akan sha’anin tsaro.
Jibrin wanda babban daraka ne a sha’anin kasuwanci na hukumar gidaje ta ƙasa ya ce duk da cewa gwamnatin jiha ta bayar da ta ta gudummawar wajen daukar nauyin dalibai, “Yana da kyau muma mu ƙara a matsayin tamu gudummawar wajen taimakawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a nan Kano.

“Ina so in saka muku ƙaimi domin ku sake zage damtse wajen neman ilimi, waɗanda ba za su iya biyawa kansu kuɗin wannan jarabawa ta NECO da NBAIS sun samu wannan dama a yau”
“Bama so mu ganku kuna yawo a titi, wannan dawainiyya ce akan duk wani dan Najeriya wajen ganin rayuwar mutane ta inganta”.
Sannan ya sake kira ga ɗaliban da suka samu wannan dama da su yi amfani da ita domin samun gobe me kyau.
Taron ya samu halartar shugabannin dalibai, shugabannin alumma, na jam’iyya da kuma masu ruwa da tsaki a fannoni da dama.