Chukuku: Ƙauye A Najeriya Da Al’ada Ta Hana Soya Ƙosai

5

Ƙosai wani abu ne da ake yi da wake wanda ya samu karɓuwa sosai a tsakanin al’ummar Najeriya da ma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

Wasu ƙabilun sukan sa wa ƙosai kifi a yayin da za a soya shi duk dan a ƙara masa daɗi.

Da yawan ‘yan Najeriya musamman Hausawa da Yarbawa na cin ƙosai ne da safe a matsayin kalaci.

Sai dai a wani ƙauye mai suna Chukuku, wanda yake dab da Birnin Tarayya, Abuja, al’ada ta hana soya ƙosai.

Duk da zamananci da yake samun Abuja— ɗaya daga cikin birane mafiya saurin ci gaba a Afirka ta Yamma,, har yanzu al’ummar Chukuku suna imani da tsohuwar al’adarsu wadda ta hana soya ƙosai a ƙauyen.

Kosai

Wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya gudanar ya gano cewa ba a haramta cin ƙosa a Chukuku ba, soya shi aka hana.

Chukuku, ƙauyen da ƙabilar Gbagyi suka fi yawa haɗi da Yarbawa, Inyamurai, Hausa da sauransu, manoma ne sosai.

Shugaban wannan ƙauye, Malam Bikko Usman, ya ce ba wani dalili da ya hana al’ummar ƙauyen soya ƙosai, kawai al’ada ce da suka gada iyaye da kakanni.

Malam Bikko ya ce amma za a iya siyo ƙosai daga wani waje a kawo Chukuku kuma a ci.

“Soya shi aka hana ba ci ba.

“Mun taso daga wani ɓangare na Chukuku zuwa nan, shi yasa har yanzu ba ma bari a soya ƙosai.

“Ba zan iya cewa me yasa aka hana ba, amma dai haka abin yake daga inda muka taso. Al’ada ce daga wata al’umma zuwa wata”, in ji shi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan