Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin Farfesa Ɗantani Wushishi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Najeriya, NECO.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya sanya wa hannu ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta ce naɗin Farfesa Wushishi ya biyo bayan rasuwar tsohon Shugaban NECO, Farfesa Godswill Obioma, wanda ya rasu wasu watanni a baya.
Ministan ya taya sabon Shugaban murna tare da kira a gare shi da ya ciyar da NECO gaba.
Sanarwar ta ce naɗin ya fara aiki ne daga 12 ga Yuli, 2021.
Farfesa Ɗantani Wushishi Farfesa ne na Kimiyyar Ilimi.
Kafin naɗinsa, Farfesa Ɗantani ya yi aiki a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya, Minna
Ana sa ran zai riƙe shugabancin NECO na tsawon shekaru biyar.
Haifaffen ƙaramar hukumar Wushishi ne dake jihar Neja.
Ku karanta Ko mene ne gaskiyar zargin da ake yi wa JAMB cewa tana rage wa ɗalibai maki?
Turawa Abokai