Babbar Sallah tunatarwa ce garemu wajen farfado da Najeriya – Atiku

130

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babbar Sallah tunatarwa ce gare mu kan me ya kamata muyi don farfado da Najeriya.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin saƙon barka da sallah da ya wallafa a shafin da na facebook a safiyar yau Talata.

“Cikin ikon Allah bikin babbar Sallah ya sake zagayowa, abu mafi muhimmanci shi ne godiya ga Allah madaukakin Sarki da Ya sake nuna mana wannan lokaci tare da iyalan mu, domin bikin wannan lokaci na sadaukarwa”

“Babbar Sallah lokacin ne dake koyar da cikakkiyar ma’anar sadaukarwa da soyayya da tuna Allah da kuma alakar mu da juna”

Alhaji Atiku Abubakar

Ya ƙara da cewa “A matsayin mu na musulmi, muna tuna labarin Annabi Ibrahim da Dan sa Isma”il amincin Allah Ya tabbata a gare su, abinda ke koya mana amincewa da dukkan al’umma a matsayin dunkulalliya”

“Muhimmancin bikin wannan rana ya zamo asalin zaman lafiya da girmamawa da yiwa juna uzuri. A matsayin mu na’yan Najeriya,, wadannan sune abubuwan da ya kamata mu yi koyi dasu, kuma mu runguma yayin da muke kokarin farfado da kasar mu daga dukkan nau’in zaman rashin yadda”

Haka kuma Atikun ya ce “Idan muka bari aka ci gaba da kisan mutanen da basu jiba basu gani ba, tare da yada akidar nuna kiyayya a tsakanin mu, ya zama tamkar bamu godewa Allah ba bisa kaunar da yakewa dukkan bayinsa”

A ƙarshe tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce “Yayin da nake mika sakon taya murna ga musulmin Najeriya da sauran sassan duniya game da bikin babbar Sallah ta bana, ina mai tunatar da mu game da fadin Annabi Muhammad SAW, da yace ” Babu wata kabila da ta fi wata a wurin Allah, amma mafi daukaka a cikin ku, wanda yafi tsoron Allah”

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na emailLabarai24@yahoo.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan