Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa Sardaunan Rano kyautar ‘Doki’

282

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa shugaban Sardaunan Rano, Honarabul Alhassan Ado Doguwa kyautar doki tare da kayan adonsa.

Dokin da shugaba Muhammad Buhari ya aikowa da Sardaunan Rano

Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, ya karɓi kyautar dokin ne a lokacin da su ka kaiwa shugaba Muhammad Buhari wata ziyara ta musamman a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Wani ɓangare na gonar shugaba Muhammad Buhari

Idan za a iya tunawa a farkon watan Yunin nan ne masarautar Rano a jihar y ta naɗa Alhassan Ado Doguwa a matsayin Sardaunan Rano kuma ɗaya daga cikin masu zaɓen Sarki na masarautar.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan