An Yi Wa Manhajar WhatsApp Kishiya A Najeriya

20

An samu nasarar sanya manhajar sabuwar kafar sada zumuntan nan ta Tabarau a cikin kundin ajiye manhajoji wato Play Store a turance.

Bayan kirkiran fitacciyar kafar sada zumuntan nan ta Tabarau, wacce ta zarce sauran kafafen sadarwa na zamani da muke dasu kamar; Facebook, Twitter Instagram da dai sauransu a wajen sauki wajen gudanar al’amuran da suka shafi harkokin sadarwa na zamani.

Kafar, wacce wani hazikin matashi masanin fasahar sadarwa dan asalin garin alkaleri dake a karamar hukumar kirfin jihar Bauchi Abdullahi Yahaya ya kirkira domin bada irin tasa gudunmawar wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da Afrika dama duniya baki daya.

Kafar, wacce ta kunshi dukkan nau’uka da sauran kafefen sardarwa suke da shi, hasalima ita ta fisu domin dukkanin abubuwan da sauran manhajojin nan guda 4 suke dashi, Facebook, Twitter, Whasapp, da Instagram dukka manhajar ta Tabarau ta tattarasu.

A yanzu dai jama’ar Najeriya, musamman ‘yan Arewa kar da ku bari a baku labari kuyi maza-maza ku garzaya play store domin sauke manhajar kafar sadarwa ta Tabarau domin samun damar bude asusu (Account) da zai baku damar gudanar da harkokinku na yau da kullum.

Kuna iya shiga nan don sauke manhajar Tabarau


Daga Comrd Zakariyah Salisu Gombe

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan