Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zama tauraron siyasar Arewacin Najeriya

107

Hukumar gudanarwa ta gidan rediyon Nagarta da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun karrama gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da lambobin yabo guda biyu.

A lokacin taron da ya ke wani ɓangare ne na murnar cika gidan rediyon shakaru goma sha biyar (15) da fara gabatar da shirye-shirye su, sun karrama gwamnan da lambar yabo mai taken “Tauraron Siyasar Arewa” da kuma wata labar girma mai taken “Barden Hausa”.

Tun da farko an karrama Gwamnan ne jim kadan bayan ya kammala hira ta awa daya a gidan Rediyon inda ya tattauna muhimman batutuwa wandanda suka shafi Gwamnatin sa tsahon shekaru shida.

A jawabin sa, shugaban hukumar gidan Rediyon Nagarta, Malam Abdulkareem Ali, ya bayyana dalilin karrama Gwamna ganduje bisa duba da yadda ya rike Jihar Kano da aiwatar da ayyukan more rayuwa da tabbatar da tsaro da kuma yadda yake tafikar da harkokin siyasar sa cikin hikima da nuna kwarewa.

A nasa ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bawa hukumar gunawar gidan Rediyon bisa yadda su ke gabatar da shiryen-shiryen su da yadda su ke kokarin hada kan al’umma da kuma yadda su ka duba chanchanta suka bashi kyautukan ban girma har guda biyu a lokaci guda, inda ya bayyana kyautar a matsayin kyautar al’ummar Jihar Kano baki daya.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group namu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan