Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Nigeria

14

Nigeria itace kasa ta farko a duniya da take dauke da mutane bakar fata sama da milyan 211 a fadin duniya.

Haka zalika a cikin wannan kasa ta Nigeria akwai ma banbantan yaruka sama da 520 da mabanbantan k’abilu guda 250, wanda kabilar Hausa Funali na ciki, sai kabilar Yarabawa da kabilar Igbo, Igala, Idoma, Ijaw, Urhobo, Ebire, Kanuri, Berum, Ngas, Ikwere, Gbagyi da kuma sauran kananan k’abilu masu tarin yawa.

Wannan kasa ta Nigeria ta sami yancin kanta daga hannun turawan mulkin mallaka a ranar daya ga watan Agusta alif 1960.

A bangaren noma da kiwo Nigeria ba a barta a baya ba domin akwai tsirrai sama da 4,700 dake fitowa ta karkashin kasa a fadin Nigeria.

Daga cikin manyan yarukan da ake amfani da su a duniya kaso bakwai cikin dari daga Nigeria suke.

A bangare na harkar shirya fina-finai namma, Nigeria tana da babbar masana’antar shirya fina-finai wadda ake kira da ” NOLLYWOOD” Wadda ita ce ta biyu wajen samar da fina-finai bayan Bollywood ta kasar India sai Hollywood wadda ita ma tana samar da fina-finai a kusan mataki na biyu.


Kuma duk da haka a Arewacin Najeriyar akwai wata masa’antar fina-finai ta Kannywood wadda ita ma tana samar da fina finai cikin harshen hausa da ake kallonsu a fadin Africa dama duniya baki daya.

Har ila yau Nigeria na dauke da manyan masu kudi na duniya kamar Aliko Dangote wanda yana da tarin dukiya sama da $Bilyan goma sha uku $13 billions.

Shahararriyar mai kudinnan ta Africa Misis Florence Alakija ita ma yar kasar Nigeria ce.

Birnin Lagos shi ne birni na farko da yafi kowacce birni yawan mutane a Najeriya, yayinda a Jahohi kuma jihar Kano ce ta fi yawan mutane gaba daya.

Abuja babban birnin Najeriya

Wani mashahurin mai zanen matoci mai suna Jilani Aliyi dan asalin jihar Sokoto a Nigeria.
Jilani shi ne babban mai zana kalolin motoci sabbi da ake kirkira a duniya kamar irinsu Chevrolet volt,

Nigeria ita ce kasa ta farko da aka fi amfani da shinkafa a duk fadin nahiyar Africa.

Nigeria tana daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki, wanda masu hasashe suke ruwaito cewar Kasar zata kasance daya daga cikin manyan kasashe ashirin a fadin duniya zuwa 2030.

Ita ce kasa mafi girma da take samar da d’anyan man fetir a Africa, haka zalika tana samar da abinci mai tarin yawa a harkar noma.

Ana yiwa Nigeria lak’abi da “Giant of Africa” ma’ana jagaban Africa sabida yawan fadin kasa da tarin al’ummar dake cikinta.

Kaso 80 cikin 100, 80% na fadin Nigeria yana yankin arewa bangaren Hausa funali kenan.

Babban zakin rubace-rubacen adabin nan kuma babban lakcara Wole soyinka shi ma dan Nigeria ne.

Daga cikin manyan littafai da aka wallafa na k’agaggun labarai akwai littafi mai suna “Things Fall Apart” daga marubuci Chinua Achebe wanda aka fassara shi sama da yaruka 50 kuma an sayar da sama da kwafi milyan goma sha uku 13M a fadin duniya.

Kadan daga cikin wasu mahimman abubuwa kenan da wannan kasa mai albarka ta kebanta dasu, wanda hakan tasa kasar tayi zarra a cikin tsarekunta.

Allah ka kara daukaka kasata Nigeria da Al’ummar dake cikinta Ameen
Fassarar rahoton #WestAfricanInsider

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan