NEPU Ta Cika Shekaru 71: Labarin Gwagwarmaya da Neman ƴancin Talaka

25

A yau Lahadi kimanin shekaru Saba’in da ɗaya (71) da wasu matasa takwas, suka hadu su takwas, a ranar takwas ga watan takwas na shekara ta 1950 suka kafa jam’iyya mai manufofi takwas ba guda daya.

A wani ƙaulin ma an ce sun yi zaman kafa wannan jam’iyya ne a gida mai lamba takwas, a Warri Street da ke cikin Sabon Garin Kano, a arewacin Najeriya.

NEPU dai na cikin jam’iyyun siyasar Najeriya a lokacin jamhuriya ta daya.

Mutum 8 da su ka kafa jam’iyyar Nepu

Koda yake jam’iyyar a yanzu bata, amma har yanzu wasu ‘yan siyasa a Arewacin kasar na bugun kirji da akidar da ta kira ‘ta fafutukar samarwa talaka ‘yanci’ daga abinda tace danniyar mahukunta a wancan lokacin.

A yanzu dai babu abinda yan siyasa da dama musamman a Jahohin Kano da Jigawa suka fi kokarin danganta kansu da su kamar jam’iyyar ta NEPU.

Har yanzu dai akwai sauran yan jamiyyar kalilan, wadanda ke raye kuma a jiya sun yi wani bikin cika shekaru sistin da kafuwar jam’iyyar.

Nepu da ‘Nehunci’ cikin shekara 71: Ina aka kwana da gwagwarmaya?

A tsakanin waɗannan shekaru abubuwa da yawa sun faru a kasar nan. A cikin wadannan shekaru saba’in, kasar ta samu ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na Kasar Ingila.

A cikin wadannan shekaru saba’in an sauya fasalin kasar inda aka kirkiri jahar Midwest a shekarar 1963; daga baya ma aka bar tsarin lardi-lardi aka koma tsarin jiha-jiha, farko a shekara ta 1967, inda aka samar da jihohi 12.

Sai kuma 1975 inda jihohin suka koma 19. A 1987 an kirkiri karin jihohi guda biyu suka zama jumullarsu 21.

A shekarar 1991 aka samar da karin wasu jihohin goma suka zama 30. Sai kuma a shekarar 1996 inda suka zama 36.

Har wa yau a cikin waɗannan shekaru 70 an samu sauye-sauye ta fuskar tsarin mulki da ma salon gudanar da mulkin. Sojoji sun fatattaki farar hula.

An yi yaƙin basasa na tsawon watanni talatin, bayan aƙalar mulkin kasar ta yi ta kara-kaina a tsakanin sojoji ta hanyar juye-juyen mulki, an kara dawowa turbar mulkin farar hula tare da sauya tsarin mulkin kasar daga wanda aka gada daga Ingila na Firaiminista zuwa salon mulki na kasar Amurka mai tsarin shugaba mai cikakken iko.

Ƙari kan waɗannan duka kuma shi ne rushe siyasar ɓangaranci da ƙabilanci ta yadda a yanzu doka ba a amince da kafa jam’iyyu da suka taƙaita ga wani sashe na kasar nan ba ko kuma jam’iyyar ta zama ta iya ƴan wata kabilar ba ne.

Domin a wancan lokacin akwai jam’iyyu irin su Borno Youth Movement (BYM) ta mutanen Borno; Ilorin Talaka Parapo (ITP) ta Yarabawan Ilorin; United Middle Belt Congress (UMBC) wacce kusan ace ta ‘yan ƙabilar Tibi ce kawai karkashin shuganban siyasarsu na lokacin Mista J. S. Tarka.

Haka misalan jam’iyyun wancan lokutan suke domin ko ita NEPU ai cikakken sunanta shi ne Northern Elements Progressive Union kuma ayyukanta kacokan da gwagwarmayar da ta yi a iya rrewacin Najeriya ne.

Tsangwama da azaba

Kusan duk lokacin da tattaunawa ta biyo kan gwagwarmayar NEPU ana ba da labari ne kan irin tsangwama da azaba da ‘yan jam’iyyar da masu goyon bayanta suka fuskanta karkashin ma su mulkin wannan lokacin.

Ba kasafai ne za ka ji tattaunawa kan gundarin gwagwarmayar tafiyar ba, ma’ana manufofin da ita jam’iyyar NEPU ta sanya a gaba ba.

Da za a yi irin wannan tattaunawar da watakila hakan zai zama manuniya kan fahimtar hakikanin gwagwarmayar NEPU.

Wacce nasara aka samu? Ya aka yi aka samu wannan nasarar? A ina aka gaza? Me ya sa aka samu wannan gazawar? A wane hali ake ciki yanzu?

A takaice, manufa da muradin NEPU su ne faɗa da tsarin kama-karya na haɗakar sarakunan gargajiya da Turawan mulkin mallaka wanda ake kira Indirect Rule, wato tsarin da su Turawa ke tasarrufi da rayuwar jama’a amma ta hanyar amfani da sarakuna waɗanda su ne suke gudanar da komai.

Don haka a zahiri sarki ke mulki amma shi ɗin ba komai ba ne face dodo-rido tun da tsare-tsare da dukkan umarni suna hannun Turawan. Aiwatarwa ce kawai aka damƙawa masu sarautar.

Lokaci ba abin da ya bari. A yau babu Turawan mulkin mallaka; sun bar mana kasar tun shekaru sittin da suka wuce.

Sarakunan gargajiya kuma a yau sun zama hoto; ba su naɗa alƙalai ba sa shari’a. Haka kuma ba su da ƴan doka da kuma gidajen yari a karkashin ikonsu.

Duk wadannan sauye-sauye sun faru a ƙarƙashin mulkin soja musamman ma a shekarun 1967 da kuma 1976.

Sai dai kuma duba na tsanaki zai nuna mana cewa bakon da ake murnar ya tafi ba fa tafiya ya yi ba. Salon yadda abubuwan suke tafiya ne kurum ya sauya.

Zalunci da kama karya suna nan zagaye da mu cikin rayuwar mu ta yau da kullum. Babban tashin hankalin ma shi ne saɓanin yadda a baya ba daidai ba take a matsayinta na ba daidai ba, a halin yanzu mun yi nisan da har ma ba daidan ba ita ake yi wa kallon daidai.

Saɓanin yadda a baya ake samun masu yin fito na fito da abubuwan ɓarna, a yau galiban mutane neman yadda su ma za su shiga cikin da’irar yin wannan ɓarnar suke yi domin su ma a rika damawa da su.

Lokaci ya nuna wasu abubuwan da NEPU ta ke kallon za su zama masu amfani ga al’umma sun rikiɗe sun zama barna.

Tsarin kananan hukumomi na ɗaya daga cikin wadannan abubuwa. An samar da kananan hukumomi dan su zamanto ma fi kusanci ga jama’a. To amma a yau babu komai ciki sai almundahana, wasoson dukiyar jama’a da babakere.

Hatta lamarin zaben shugabannin kananan hukumomin ya zama wasan yara. Wannan abu ne da kowa ya sani ba sai an faɗa ba.

Wani karin misalin shi ne tabbatar da damar yin zaɓe ga kowa da kowa. Jam’iyyar NEPU ta yi adawa matuƙar adawa da tsarin zaben hawa-hawa saboda son ran da ake aiwatarwa karkashinsa.

A karshe dai an dawo zaɓen falle daya a shekarar 1959. Mata kuma sun fara jefa kuri’a a shekarar 1979.

Sai dai kuma wannan tsarin cike yake da damuwa. A wannan tsari da kare da rago duk darajar su daya. Maimakon sanin ciwon kai ya zama shine abun dubawa wajen kyale mutum ya zabi wadanda za su tafiyar da al’amuran kasa, sai kawai aka ce shekarun haihuwa kadai sune abun dubawa.

A karkashin wannan tsari da hamshakin dan kasuwa mai masana’antu da kuma gafalallen matashi mai yawo kwararo-kwararo yana shaye-shaye da addabar jama’a duk matsayin kuri’arsu daya.

Saboda haka waɗannan gafalallun matasa sune da kunzumin kuri’unsu za su zaɓo baragurbin da zai zo ya dagula sha’anin tattalin arzikin kasa ta yadda wancan mai masana’antu zai durkushe! Ya Ilahiy ina hikima cikin wannan?

Mallam Aminu Kano

Jagora kuma shugaban jam’iyyar NEPU, Mallam Aminu Kano, yana cewa babbar nasararsa a duniya ita ce koyawa talaka cewa ‘na ki’, ‘ban yarda ba’, ‘ba haka za ai ba’. Sai dai bisa ga dukkan alamu Talaka ya manta da wannan karatun tuntuni.

Mallam Aminu Kano

Yanzu kirarin da ake yi wa kusan kowane dan siyasa shi ne ‘kowa ya bi’.

Kuma wannan shi ne gaskiyar lamarin. A yau in ka ga ba abi dan siyasa ba to bai saki tsaba ba ne.

Domin kuwa kaza a kullum mai zuba tsaba take bi. Ya ishe ka misali cewa lokacin da shi Mallam Aminu ya fito takarar zuwa majalisar taraiya ai abin da ake cewa shi ne:

”Birni da kauye, mu zabi Aminu dan Talakawa”

Amma yanzu abin da za ka ji ana cewa shi ne: ‘dan Sarki jikan Sarki! ko kuma wani abu makamancin haka.

Saboda haka duk abubuwan da NEPU ta yi gwagwarmaya kan su suna nan tare da mu har zuwa wannan lokaci. Illa iyaka sun sauya kama. Duk da cewa yanzu Turawan mulki sun tafi to amma fa har zuwa wannan lokaci tattalin arzikinmu a hannunsu yake.

Duk da cewa an karbe duk wani iko daga sarakunan gargajiya to amma fa har yanzu akwai kashin dankali, danniya da kama karya.

A zancen gaskiya ma abubuwan kara munana suka yi. A yau ana kamawa a ɗaure haka kurum. Shari’a ta zama tamkar ciniki.

Mafitarka kawai shi ne me ka ke da shi me kuma za ka bayar. Ana kashewa ana daukewa har ma a ɓatar da mutum ba tare da an yi wani abu akai ba.

Rayuwar mutane na cikin haɗari. Babu tsaron rayuka, dukiya da ma mutunci. Maganin abu a kasar nan shi ne kawai kar ka bari a yi maka, domin matukar an yin to fa ruwa ya sha.

Kamar yadda na fada har yanzu muna fama da kashin dankali. A halin da ake ciki yanzu a kasar nan abin lura kawai shi ne wa ka sani wa ya san ka, ko kuma wa ka sani wanda ya san wani. Sai ka ba da kuɗi za ka samu aikin yi.

Sai ka ba da kudi za ka samu karin girma a wurin aiki. Kai ko da barin aikin ka yi to fa sai ka biya wani abu sannan haƙƙoƙinka na ma’aikaci za su fito.

Haka abin yake hatta a fannin shugabanci da siyasa: sai ka ba da kudi za ka samu takara; sai ka ba da kudi za a zaɓe ka. Haka ma in wani muƙami ne za ai maka a cikin gwamnati to fa shi ma sai ka biya!

A irin wannan yanayin ya zaka yi tsammanin ma’akacin gwamnati ya zamo mai kwazo da jajircewa kan aikinsa? A irin wannan yanayi ya za ka tsammaci ɗan siyasa ya damu kansa da damuwar al’umma?

Saboda haka gwagwarmayar NEPU ba ta cimma gaci ba. Har yau ba a je inda akai kuɗurin zuwa ba.

Wannan kuma ba ɓoyayyen abu ba ne ga duk wanda ya san haƙiƙanin tarihin tafiyar domin tun a wancan lokacin ɓaraka ta samu ta yadda dukkanin matasan nan guda takwas da suka kafa ta sai da suka fita daga cikinta. Wasu suka koma abokiyar hamaiyarta wato NPC.

Wasu suka koma aikin gwamnati yayin da wasu kuma suka koma gefe suna gudanar da sha’anin rayuwarsu ta wasu fannonin daban-daban.

Maimakon taruwa kowace shekara, taro bayan taro, ana bayar da labarun su Tsalha Ɗankasa, Malami Ƙoƙi, Sahabi Sokoto, Illa Ringim, Inuwa Buraji da sauransu, abin da ni nake ganin ya fi kyautuwa shi ne mu yi sabon ƙoƙarin tantacewa, tsefewa tare da tsara yadda gwagwarmayar NEPU ko kuma ‘Nehunci’ zai kasance a Nijeriyarmu ta yau.

Gwagwarmayar a yanzu ba ta fito na fito da sarakuna ba ce. Su ma ta kansu suke yi yau! Ba kuma da Turawan mulkin mallaka ba ne.

Alal haƙiƙa gwagwarmayar da ake bukata a Najeriyar yau shi ne sauya tunanin Talakawa ta hanyar fito da su daga dimuwar da ‘yan siyasar mu suka jefa su ciki ta yadda a yau ya zama Talaka bai ma san kan sa ba.

Babban abin tashin hankalin ma shi ne su wadannan ‘yan siyasar na yau a cikinsu akwai ‘ya’ya da ma jikokin NEPU. Kuma har zuwa yau suna iya tutiya ko da’awar cewa su ma ‘yan NEPU ne ko kuma akwai jinin NEPU a jikinsu. To amma fa duk karya ce ihun kawai!

Wannan maƙala ce ta musamman daga Sunusi Umar Sadiq, lauya kuma mai sharhi kan lamurran yau da kullum da ke Kano, ya rubuta ta a shekarar 2020.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan