Wasika Zuwa Ga Sarkin Musulmai Alh. Sa’ad Abubakar kan Malamai Masu Wa’azi

246


Na fara Wannan rubutu da sunan Allah Mahaliccin kowa da komai. Tsira da aminicin Allah su Kara tabbata zuwa ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da Sahabbansa baki dayansu. Kuma muna Kara wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi fatan alheri akan kokarinsa ga taimakon addini da fadar gaskiya bakin gwargwado. Allah ya kara maka lafiya da hakuri da kuma Imani Ameen.

Bayan haka, Muna kira zuwa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi da yayi amfani da matsayin da Allah ya bashi na Shugabancin Musulmin Nigeria ya dauki matakai na hukunta duk wani Malami ko Limaman da zasu rika labewa da sunan wa’azi, ko kungiyanci, ko limanci ko mumbarin wa’azinsu suna cin mutunci ,da zagi da kuma aibanta junansu ko Malaman da ba su shiri da su.

Muna tunatar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi cewa, yanzu fa mafi yawan Malaman mu a Nigeria sun maida munbarinsu wurin zambo da aibanta juna, da kuma zage-zage, da kazafi, da yada sauran kalaman da ba su da dadin saurare ga duk wani mai tsoron Allah .

Wannan Yana gurbata tarbiyar samari, da sauran matasa ko daliban ilmi dake tasowa ko sauraren ire-iren wadannan Malamai masu zagin mutane ko wanda duk ya saba ma ra’ayinsu ko kungiyarsu, ko da son ra’ayoyin nasu sun saba ma na wasu magabata .


Bugu da kari skan samu daga cikin wasu Malamai suna maida munbarinsu tamkar dandalin munbarin siyasa da cin mutuncin juna akan wadanda suke da sabanin siyasa da su.


Bai kamata ga mai Alfarma Sarkin Musulmi da Mukarrabansa kamar Supreme Council for Islamic Affairs su sa ido har su ki daukar matakai na Shari’a akan irin wadannan abubuwa na cin zarafin juna a wurin wa’azi ko munbarin masallatai.

Irin zage-zage,da sauran alfasha na cin zarafin da wasu Malamai kewa junansu har mabiyansu na dariya ya ci karo da gargadin Alkur’ani a cikin Suratul Nahll da kuma Suratul Hujuraat inda Allah yace ayi wa’azi da hikima ba tare da an aibanta juna da miyagun lakabobi ba.

Daga karshe muna Kira ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi da ya kafa wani Babban Kwamiti a kowace jiha da local government wadanda zasu rika sa ido zuwa ga wa’azozin Malamai da hidubobinsu domin magance ire-iren wadannan rashin hikima a wurin wa’azi.

Idan har ankama Malami da laifin sabama ladubban wa’azi akan son rai sai a ladabtar da Shi ko a canza Shi ko wane jiha yake limanci a Nigeria.


Babbar Matsala da mafi yawan Malamai ko limamai ke fuskanta shi ne dalibansu da ke saurarensu ba su fada musu gaskiya idan suka wuce gona da iri gA wa’azozin su sai dai suyi ta yi musu kabbarori a munafunce.


Daga karshe, musan cewa Musulunci da Musulmin Nigeria suna da hakki na kulawa da tsawatarwa idan har aka aikata cin mutunci gare su ko aka maida masallatai ko kungiyoyi dandalin raba kan Al’umma . Hatta kiristoci ba su cin zarafin junansu kamar yadda wasu daga cikin Malaman suke yi a Nigeria .

Da fatan Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai kula da aiwatar da wadannan shawarwari a duk fadin Nigeria don ya zama abin koyi . Muna rokon Allah ya datar da mu da jin tsoronsa da kuma bautarsa akan gaskiyya da iklasi .

Allah ya kawo mana karshen musibun da ke damun Nigeria, musamman Arewacin Nigeria da sauran Musulmin duniya. Amin.

Daga shafin Sheikh Hussain Yusuf Mabera

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan