Fitila: Manyan Rahotannin Da Yan Jarida Suka Rawaito A Makon jiya

26

A makwon da mu kayi ban kwana da shi an rawaito labaru masu ɗaukar hankalin al’umma a bangarori da dama, amma labarin da ya fi ɗaukar hankalin al’umma musamman masan diflomasiya shi ne wanda wasu jami’an tsaro suka ci zarafin wani ma’aikacin diflomasiyan Najeriya wato Muhammad Buba a ƙasar Indonesia.

A fefen bidiyon da aka ringa yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani, anga inda jami’an tsaro suke cin zarafin jami’in inda suka danne shi tare da dora gwiwowin su akan wuyansa.

Jami’an tsaron Indonesiya suna cin zarafin ma’aikacin diflomasiyan Najeriya

Wannan al’amari dai ya jawo cece-kuce wadda har ta kai ministan harkokin wajen najeriya wato Jeffory Onyeama ya fitar da sanarwa tare da gargadi ga ƙasar, wannan yasa gwamnatin ƙasar nan take ta fitar da takardar bayar da hakuri ga hukomin Najeriya.

Sai dai ƙungiyar tsofaffin wakilan Najeriya a ƙasashen waje sunyi Allah wadai da abinda ya faru sannan suka yi kira ga Najeriya da ta kori wakilin ƙasar Indonesia da ke Najeriya sannan ta dawo da wakilinta dake ƙasar ta indonosia Najeriya.

Wannan al’amari dai a wurin masana diflomasiya suna ganin cin mutunci ne ga Najeriya musammanma yadda ita ƙasar tayi ƙaurin suna wurin cin zarafi da take hakkin al’umma musammama baƙaƙen fata yan Nahiyar Africa.

Kiran mu a nan shi ne Najeriya ya kamata ta ɗauki tsautsauran mataki game da wannan batu domin kare afkuwar makamacin wannan nan gaba don in har waɗannan jami’ai zasu iya aikata wannan cin zarafi ga ma’aikacin difilomaciya to ya kuma ga sauran al’ummar Najeriya da suke ziyatar wannan ƙasa domin kasuwanci da sauran al’amura.

A ɓangaren tsaro kuma labarun da suke fitowa daga jihar Niger suna nuni da cewa masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da kwamishinan yada labarai na jihar a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida. Wannan batu dai ya tayar da hankalin al’umma musamman duba da matsayi na shi wanda aka yi garkuwa da shi duk da dai an samu labarin kuɓutarsa.

Ko a satin daya gabata wannan shafi yayi tsokaci game da yadda aka sace mahaifiyar kakakin majalisar jihar Zamfara wadda har a wannan lokaci ba a samu labarin sakin ta ba.

A dai wannan makon ne yan bindigar da suka addabi al’ummar yankin Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger da sauran sassa na Arewacin Najeriya sun harbe tsohon kansilan mazabar Sankalawa-Sabon Gida a karamar hukumar Bugudu a jihar Zamfara har lahira a cikin gidansa ba tare da daukar komai ko yin garkuwa da wani ba.

Haka ma dai a dai jihar ta Zamfara yan bidigar sun sace matar wani tsohon kansilan mazabar Babangida Damba, Hassan Sadauki tare da jaririnsu ɗan wata takwas (8). Waɗannan batu dai suna nema su gagari Kundila duk da kokarin da jami’an tsaro ƙasar nan suke yi domin su dakile su.

A dai wannan mako ne tsohon Sarkin kano, Muhammadu Sunusi II yake cika shekara 60 a duniya. Wannan ne yasa domin godiya ga Allah da tsowon ran da sarki yayi da kuma murnar cika shekaru sittin ɗin Sarkin tare da wasu manyan abokansa da magoya bayansa suka shirya wata kwaryakwaryar taro tare da lakcoci.

Muhammadu Sunusi II

Amma ba wannan batu ne yake daukar hankalin al’umma ba musamman masu fashin baƙi a kafafen sada zumunta na zamani sai wata takarda da ka fita a yamacin ranar juma’a wadda wannan shafi bai tantance sahihancinta ta ba dake nuni da cewa gwamnatin jihar ta kaduna ta baiwa tsohon Sarkin gudunmawar naira miliyan 25 domin shirya taron.

Wannan batu dai ya yamutsa yazo inda wasu suke ganin hakan da akayi yayi daidai, wasu kuma suke ganin abinda akayi ɗin bai dace ba duba da irin halin matsin rayuwar da al’umma suke ciki a wannan yakin namu.

Masu tunanin cewa bai dace ba suna ganin yafi dacewa ace gwamnatin tayi anfani da wannan kudi wajen yiwa al’umma aiki wadda alhakin yin hakan ya rataya akanta duba da irin halin rayuwa da ake fama dashi.

To komai wannan shafi zai ce game da wannan batu, a haƙiƙanin gaskiya bai kyautu ace an ɗebi kudin al’umma na jiha in har hakan ta tabbata anyi wani abu daban ba, in mu kayi duba da wanene shi tsohon Sarkin da irin abokansa zamu ga cewa dukkaninsu attajirai ne masu hannu da shuni wadanda wannan abu ma sunfi karfinsa, wadda mutum daya ma a cikinsu zai iya fitar da wannan kudi ba tare da yaji ko bincini a jikinsa ba.

Har kullum dai kiran wannan shafi shi ne mahukunta su hankalta su san hakkin al’umma Allah ne ya dora musu kuma zai tambaye su ranar gobe kiyama.

Rahotannin da ke fitowa daga ƙasashen ƙetare na nuni da cewa mayaƙan ƙungiyar Taliban sun ci galabar kwace fiye da birane 5 a kasar Afghanistan, wannan al’amari masana harkokin waje suna ganin ɗan lokaci kankani ne ya rage wa ƙungiyar ta kwace ikon mulkin kasar.

Taliban

Idan zamu iya tunawa kimanin shekaru 20 da suka wuce ne mulikin ƙasar ya bar hannun ƴan Taliban ɗin lokacin da sojojin haɗin gwiwa bisa jagorancin sojojin Amurka suka taimakawa masu sausauƙan ra’ayin wurin karɓar mulkin kasar.

Tun lokacin yan ƙungiyar suke ta neman dawowa mulkin ƙasar amma hakan ya gagara saboda kasancewar sojojin haɗin gwiwar da na Amurka sun yada sannani a ƙasar.

To amma a shekarar 2020 anyi wata yarjajjeniya da ƙasar ta Amurka a ƙasar Qatar domin sojojin haɗin gwiwar bar kasar.

Shin manene makomar wannan kasa idan yan Taliban suka sake karɓe ta?

Wasu na ganin ƙasar zata samu koma baya, yayin da wasu kuma suke ganin tun farko dama katsa landan da ƙarfaƙarfa aka yi musu a matsayinsu na ƙasa mai cikakkiyar iko.

Filin Jan Hankali:

A wannan makon wannan fili zai yi duba akan abubuwa guda 3 wanda ya kamata al’umma su kula da su sosai.

Na farko waccan satin munyi tsokaci game da annobar amai da guduwa wadda har yanzu ake ta fama da ita a wannan yanki na Arewacin Najeriya, kiran wannan fili har kulum dai shi ne al’umma su lura da irin abincin da suke ci da kuma ruwan da suke sha, sannan su zama masu tsaftace muhallin su da abincinsu ako da yaushe domin gujewa kamuwa da wannan cuta.

Abu na biyu kuma shi ne, duk da hukumar lafiya ta kasa ta fitar da sanarwa cewa ba ta tunanin sake kulle gari akan yawaitar karuwa da kamuwa da cutar sarkewar numfashi wacce aka fi sani da Covid-19, yana da kyau al’umma su lura sosai sanna su rinƙa bin dukkanin sharuɗɗan da hukumar lafiya ta sanya kamar yawaita wanke hannu, bayar da tazara da saka takunkumin baki.

Tabbatarwa ana bin wadannan shawarwari shi zai kare al’umma daga kamuwa daga wannan cuta musamman sabuwar nau’in cutar da ta addabi duniya yanzu wacce ake kira da Delta Varient, kamar yadda masana suke ce ita wannan nau’in tafi ta baya saurian kisa da kuma yaduwa. Allah ubangiji ya kare mu.


Sai abu na 3 kuma na karshe shi ne karin kira game da ambaliayr ruwa da ke hallaka al’umma tare da dukiyoyinsu. Ko a wannan mako an samu rahoton cewa ambaliyar ta haifar da asarar rayuka guda biyar sannan ta lalata gonaki fiye da 1,565 a jihar Bauchi.

Kiran wanna fili shi ne al’umma ya kamata su rinƙa ɗaukar shawarar masana yanayi, su guji yin gine gine a kusa da mugudanan ruwa da zubar da shara, mutane da suke zaune a kusa da gaɓar ruwa su ƙauracewa wuraren, sannan ita kuma uwa uba gwabnati ya kamata tayi duk mai yiyuwa domin kare al’ummarta daga wadannan masifu, sannan wadanda wannan abu ya shafa ta tallafa musu.

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan