Kisan da aka yiwa matafiya a jihar Filato ta’addanci da dabbanci ne – Femi Fani Kayode

353

Tsohon ministan zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya, kuma Sadaukin Shinkafi, Mista Femi Fani Kayode ya bayyana kisan da ƴan ta’addar Irigwe su ka yiwa wasu matafiya a jihar Filato a matsayin dabbanci da kuma ta’addanci.
Femi Fani – Kayode ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook a safiyar yau Lahadi.

“Yan tada zaune tsaye daga ƙabilar Irigwe a Jos sun kashe matafiya a ƙalla sama da 40 yayin da suke dawowa daga jihar Bauchi bayan sun halarci taron addini a jihar Bauchi jiya”

Femi Fani – Kayode

“Wannan ta’addanci ne. Rashin imani ne. Kuma tsagwaron hauka ne. Waɗannan ƴan ta’adda tabbas sun nuna cewa ba su da wani buri face masu son zubar da jini, masu tunani kamar dabbobin” In ji Femi Fani – Kayode.

A jiya ne dai wasu ƴan ta’adda su ka kashe wasu matafiya aƙalla mutum 30 tare da jikkata wasu da dama a Jos babban birnin Jihar Filato

Femi Fani-Kayode dai ya shahara a wurin yin sharhi kan al’amuran yau da kullum a Najeriya a duk kafar da ya samu, inda a lokuta da dama ke yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da Hausawa.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan