Sanata Nasiru Ibrahim Mantu ya rasu

133

Wasu rahotanni daga jihar Filato sun bayyana cewa Allah ya yiwa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar nan Sanata Nasir Ibrahim Mantu rasuwa a cikin safiyar Talatar nan.

Tun da farko jaridar Leadership ce ta rawaito rasuwar tsohon dan majalisar dattawan.

Sanata Nasiru Ibrahim Mantu

Haka kuma Nasiru Mantu fitaccen dan jam’iyyar PDP ne wanda a lokuta da dama aka zarge shi da hannu wajen cuwa-cuwar siyasa, ciki har da zargin yunkurin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai bai wa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo damar yin ta-zarce a karo na uku.

Sai dai shi da Cif Obasanjo sun sha musanta zargin.

Hakazalika Sanata Mantu ya taɓa zama Amirul Hajji a zamanin mulkin Mr Obasanjo.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan