Shekaru 6 na mulkin shugaba Muhammadu Buhari: Abubuwa 7 da ƴan Najeriya su ka rasa

  28

  INA tunatar da Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo cewa nauyin da suka dauka a wuyansu ga jama’ar Najeriya shi ne zasu yi mulki na adalci kuma kowa zai ji dadin mulkinsu, za a samu sauki da walwala, zasu samar da tsaro da aminci a kasa, za su baiwa marasa aikin yi aiki da sana’a, zasu yi yaki da cin hanci da rashawa , sannan za su gyara tattalin arziki.

  NI A FAHIMTATA shekara shida da wata uku na APC da PMB da PYO da sauran aiki JA a gabansu. Ya kamata su san cewa:

  Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osibanjo

  -Babu tsaro a ko ina

  • Darajar Naira kullum faduwa take
  • Farashin kaya Hawa yake
  • Bashin da ake ci ninkawa yake
  • Hadurra akan hanya kisa suke
  • Kuɗin shiga na hukuma baya yake
  • Abubuwa tabarbarewa suke

  Muna cikin jam’iyyar APC, muna kira ga APC, A JI tsoron Allah, a saki layin da ake kai wanda ba zai dore ba, A kama sabon layi da zai dore kuma ya ceto Najeriya.

  Bello Muhammad Sharada hadimi ne na musamman ga Sanata Malam Ibrahim Shekarau

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan