Fitila: Sukuwa Da Zamiyar Yan Jarida A Makon Jiya

596
Ali Sabo


A yau zamu yi duba kan wasu manyan al’amuran da suka faru a bangaran tsaro a wannan kasa tamu wanda ya dauki hankalin al’umma musamman musulmai yan Arewa, wannan abu ya ta da hankali duk wani mai sauran tausayi a zuciyarsa.

Na farko dai abinda zamu yi duba akansa shi shi ne kisan gillan da aka yi wa wasu matafiya ashirin da biyar (25) akan hanyar Jos lokacin da suke komawa daga wani taron addu’a wanda darikar Tajjaniyya karkashin jagorancin shehin malamim nan, Sheik Dahiru Usman Bauchi ta shirya a garin Bauchi.

Matafiyan wadanda akasarinsu yan jihar Osun ne sun gamu da ajalin nasu ne a lokacin da wasu samari yan ta’adda yan kabilar Irigwe suka tare su a hanya suka yi musu kisan gilla.

Ku karanta: Fitila: Me Kafafen Yada Labarai Su Ke Cewa A Makon Jiya

Kawo yanzu dai mahukunta sun kama akalla mutum talatin wadanda suke da hannu akan kisan, sannan sun bazama neman wadanda suka bata ba a gani ba.

Wannan al’amari dai ya haifar da cece-cuke game da yadda mutanan wannan kabila suke cin karen su babu babbaka kuma an kasa daukar mataki akansu.

Ko a baya ma in zamu iya tunawa anyi wa wani babban soja da ake kira da General Alkali kisan gilla a wannan yanki kuma har kawo yanzu gwamnati ba ta dauki wani mataki kwakkwara akan batun ba.

Sai dai bayan faruwar wannan al’amari an jiyo muryoyi da dama suna Allah wa dai da wannan kisa da kuma kira da kakkausar murya na cewa gwamnatin tarayya ta dauki mataki mai tsauri akan wadanda suka aikata wannan abu, kamar yadda wani fefen bidoyo yake yawo dake nuni da Sheik Dahiru yana wata waya inda aka jiyo shi yana cewa idan muhukunta ba zasu iya kare al’umma ba da su sauka su bawa wadanda zasu iya kare al’umma.

Wannan irin magana dai ba yanzu aka fara yin ta ba, inda masana da al’ummomi da ban da ban suke ta kiraye-kiraye ga masu rike da madafun iko da su sauka daga mukamin su matsawar ba zasu iya kare dukiyoyi da rayukan al’umma ba.

Sannan a dai wannan mako ne yan bidiga a jihar Zamfara suka yi awon gaba da daliban makarantar koyon aikin gona dake garin Bakura. Al’amarin da ya faru a daren ranar Lahadin da ta gabata, jaridar BBC ta rawaito cewa yan bindigar sun sace mutane goma sha tara (19) ciki har da wani malami da matarsa da kuma ‘ya’yansa guda biyu. Sannan an samu rahoton asarar rayuka ta mutum uku ciki harda jami’in dan sanda mai mikamim sufeto.

Satar dalibai a jihar ba sabon abu bane idan muka yi duba dacewa ko a kwanakin baya yan bindigar sun sace daliban makarantar kimiya ta mata dake garin Jangebe wadanda sai da aka akai ruwa rana kafin kubutar da su daga hannun yan bindigar. Wadannan batu dai sun dade suna tsonewa al’ummar wannan yanki ido kuma sun sha kokawa amma shuwagabanni sun toshe kunnuwansu da kuma nuna halin ko in kula ga al’amarin.

A gaskiya wadannan abubuwa da suke faruwa a wannan yanki na Arewa suna tayarwa al’ummar yankin hankali musamman masu karamin karfi, inda in muka yi duba zamu ga cewa dubunnan al’umma sun rasa rayukansu sannan wasu sun rasa matsugunnansu, an mai da su yan gudun hijira, sannan yara da dama an mai da su marayu.

Haka ma dai, a wannan bangare na tsaro a jahar Katsina an jiyo gwamnan jahar, Aminu Bello Masari yana sanar da al’umma jihar da su ta shi tsaye su kare kansu daga harere-hareren ‘yan bindiga. Wannan sanarwar ta gwamnan ta girgiza masana tsaro da masu sharhi kan harkokin tsaro inda suke ganin cewa tabbas gwamnati ta gaza in har dai zata fadawa al’umma su tashi su kare kansu da kansu.

Aminu Bello Masari

Rikicin cikin gada ya sake barkewa a Jam’iya mai mulki wato APC a Najeriya, wannan jam’iya dai ta dade ta na fama da rikicin cikin gida tun lokacin da su wasu gwabnoni sukayi gangami suka kulla manakisar korar tsohon shugaban jam’iyar wato Comrade Adams Oshomole sannan aka bawa tsohon sakataren jam’iyar wadda shi ne gwabnan Yobe a yanzu wato Mai Mala Buni.

Masana harkokin jam’iyu da kuma harkokin shari’a sun ta tofa albarkacin bakinsu game da sahihancin rikon kwaryar da aka bawa Buni. Masanan na cewa a dokar jam’iyar APC ba yadda za’ayi mutumin da yake rike da wani mukami na daban ba tare da ya ajiye wannan mukamin ba sannan a ba shi shugabanncin jam’iyar.

Game da wannan batu dai kotuna daban-daban sun ba da fashin bakin su inda wasu suke game rikon kwaryar haramtaccene wasu kuma suke gani cewa ya halatta.

Ko ma dai menene, jam’iyar a yanzu ta shiga tsaka mai wuya musamman tun da aka fara maganar zaben shuwwabannin jam’iyar inda ko a zaben shuwagabannin mazabu da aka gabatar a wannan wata an samu rarrabuwar kai.

Mai Mala Buni
Gwamnan Yobe Mai Mala Buni

Jihar Kano tana daya daga cikin jahohin da ake samun rikicin cikin gida, kuma an sami labarin cewa tsagi guda biyu na jam’iyar sun gudanar da zaben su daban daban.

Wannan tsaguna dai sun hada da wanda mai girma gwabnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yake jagoranta da kuma wadda Dan Majalisa mai wakilitar karamar hukumar Birni a majalisar tarayya wato Sha’aban Sharada da dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa da Tofa wadda daga nan ne Gwamnan jihar ya fito wato Abdulkadir Jobe suke jagoranta sun gudanar da zabubbukansu daban daban.

Sai kuma wata kura wadda ta taso a jam’iyar wacce aka fi alankatata da tsagin mai gwamnan Kanon, inda aka jiyo mai dakin gwamnan tana wani jawabi wanda ke nuni da cewa sun fitar da dan takarar da zai gaji gwamnan jihar. An dai jiyo maidakin gwamna Farfesa Hafsat Umar Ganduje wacce aka fi sani da Gogggo na cewa wanda ya dace ya gaji gwamnan jihar Kano a zabe mai zuwa shi ne irinsu Murtala Sule Garo wato Kwamishinan Kananan Hukomomi na jihar.

Tuni dai gwamnatin ta fitar da wata sanawarwar inda take cewa yan jaridar da suka rawaito labarin basu fahimci sakon da maidakin gwamnan take son isarwa ba. To koma dai menene zamu jira mu ji yadda zata kaya a jam’iyar lokacin zaben shuwagabannin.

Kasashen Ketare

Labaru daga kasashen ketare na nuni da cewa a ranar daren lahadin da ta gabata ne mayakan Taliban su ka kwace ikon mulkin kasar Afganistan bayan sun shafe shekara ashirin basa mulkin kasar. Wannan nasara ta samo asali ne bayan yarjajjeniyar da aka kulla da kasar Amurka a Birnin Doha a shekarar alif dubu biyu da asharin inda kasar Amurkan ta kwashe dakarunta wadanda ta jibge a kasar suke tallafawa gwamnatin da suka kafa tsawon shekara ashirin.

A wani jawabi da shugaban Amurka wato Joe Biden ya fitar a ranar talata yana cewa Amurka bazata ci gaba da yakin da ba nata ba a kuma lokacin da sojojin kasar suke tsarewa. Sannna ya kara da cewa sun shafe tsawon shekaru suna horar da sojojin Afghanistan da basu makamai na zamani wadda ‘yan Kungiyar mayakan Taliban basu dashi amma suka bari a cikin yan kwanaki aka kwace kasar ba tare da sun tabika wani abun azo a gani.

Joe Biden

Wannan batu na Afghanistan dai ya tayarwa da duniya hankali sosai inda al’umma da masana da dama suke tofa albarkacin bakinsu game da makamor wannan kasa duba da wasu hotuna da bidiyo da suke yawo a gidajen yada labarai na talabijin da kafafen sadarwa da ke nuni da wasu al’umma kasar a filin jirgin tashin jirage na babban birnin kasar wato Kabul suna turereniya domin barin kasar wadda har rahoto ke nuni da cewa an samu asarar rayuka da dama ciki harda wata mai dauke da juna biyu da wani matsahi da ya taba buguwa Kungiyar kallon kafar kasar.

Duk da sanarwa da mayakan Taliban din suke bayarwa na cewa sun yafewa kowa ba zasu yi bita da kulli ba amma al’ummar kasar suna shakku akan haka.

A wani labari da gidan talabijin na Aljazeera ya fitar a ranar Alhamis yana nuni da cewa Yan Kungiyar Taliban din sun fara farautar wasu mutane da suka yiwa sojojin NATO and Amurka aikin a baya wadda wannan labari ke cin karo da alkawarin da suka dauka nayin afuwa da kuma manta abinda ya faru a baya.

To koma dai menene zamu jira muga kamun ludayinsu.

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan