Baki Shi Kan Yanka Wuya: Martani ga kalaman jaruma Umma Shehu akan hukumar Hisba

  46

  Wannan yarinya ƴar wasan kwaikwayo ta yi rashin kunya, ta yi rashin mutunci, ta yi rashin ladabi, ta munana lafazi, ta tallata jahilci da tarbiyyar gidansu a kalaman da ta yiwa Hukumar Hisbah ta jihar Kano, kuma bai kamata su zuba mata ido ba. A ina aka ce hana ɓarna shiga tsakanin bawa da Allah ne? Yanzu sai mutum ya yi kisan kai ko ya sha giya ko ya yi sata ko yayi munafunci, duk waɗannan kaba’ir ne da Allah ya hana, shi ke nan sai a zubawa mutum ido a ce ai tsakanin shi da Allah ne? To menene amfanin kotu (Court), da alƙalai, da jami’an tsaro da gidan yari?

  Jaruma Umma Shehu

  A ƙasashen waje ƴan wasan kwaikwayo suna yin laifi ana hukunta su, ba za ka taɓa ganin wani jarumi ko jaruma sun fito suna ƙalubalantar hukuma akan tuhumar da ake masa ba. Yanzu haka a Amurka, shahararren mawaqin nan R. Kelly na fuskantar tuhuma akan zargin shi da ake da sex trafficking da bribery. A iya labaran da na ke bi ban ga wani mawaƙi ko mawaƙiya sun fito suna ba shi kariya ko zagin court ɗin da ke tuhumar da ba. Duk da ƙaurin suna da Amurkawa suka yi wajen zagi da tsiya da rashin tarbiyya.

  Ya kamata hukumar gudanarwa ta Kannywood ta ringa jan hankalinta yayanta wajen tsoma baki akan taƙaddamar da ake yawan samu tsakanin su da hukumar tace fina-finai ko kuma Hisbah. A iya bibiyar da na ke yiwa jaruman Kannywood ban ga yarinya mara kunya da ta fito fili ta ci mutuncin hukuma kamar wannan yarinya ba. Amma ban yi mamaki ba, yarinyar da ba ta san wacce ta shayar da Manzon Allah (S.A.W) bayan rasuwar mahaifiyarsa ai za ta yi fiye da haka.

  Aisar Fagge malami ne a tsangayar koyar da aikin jarida na kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kano, kuma mai yin sharhi akan al’amuran da su ka shafi Ilimi, ya rubuto daga Kano

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan